✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da ya sa Umaru Dikko ya yi kaurin suna a Jamhuriyya ta Biyu

A safiyar ranar Talata da ta gabata ce Allah Ya yi wa tsohon Ministan Sufuri a Jamhuriyya ta Biyu Alhaji Umaru Dikko rasuwa a wani…

A safiyar ranar Talata da ta gabata ce Allah Ya yi wa tsohon Ministan Sufuri a Jamhuriyya ta Biyu Alhaji Umaru Dikko rasuwa a wani asibiti a birnin Landan da ke kasar Ingila.
Alhaji Umaru Dikko wanda ya rasu yana da shekara 78 a duniya dan siyasa ne da ya yi suna matuka a lokacin mulkin Jam’iyyar NPN ta Shugaba Shehu Shagari. Yana daya daga cikin ’yan siyasar da suka tsallake kasar nan bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Alhaji Shehu Shegari a 1983.
Marigayi Umaru Dikko babban amini ne kuma mashawarcin tsohon Shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari, inda ya yi Ministan sufuri a daukacin zangon mulkinsa daga 1979 zuwa 1984.
Marigayin ya fara shiga harkokin mulkin kasar nan ne a 1967, lokacin da aka nada shi kwamishina a tsohuwar Jihar Arewa ta Tsakiya, (yanzu Jihar Kaduna). Kuma ya taba zama sakataren kwamitin da Janar Hassan Katsina ya kafa domin hada kan ’yan Arewa bayan juyin mulkin 1966.
A 1979 aka nada shi Daraktan Kamfen din neman shugabancin kasar nan na Jam’iyyar NPN inda ya samu nasarar kawo Alhaji Shehu Shagari gadon mulki.
Ya taka rawar gani a Jamhuriyya ta Biyu a matsayinsa na Ministan Sufuri kuma shugaban Kwamitin Cika-Aiki na Shugaban kasa kan shinkafa. Kuma ya kasance mai fada a ji a zamanin Gwamnatin Shehu Shagari, wanda surukinsa ne.
Kuma a lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin Shagari a karkashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari kwana biyu a gadon mulki sai Buhari ya bayyana jerin wasu zarge-zarge da ake yi wa jami’an gwamnatin da suka kifar na aikata miyagun laifuffuka. Sunan Umaru Dikko ya kasance a sama inda aka zarge shi da almubazzaranci da miliyoyin Dalolin Amurka na ribar cinikin man fetur.
Duk kokarin da aka yi don gano inda yake, Umaru Dikko ya yi layar zana, inda a karshe ya bayyana a Ingila ya zauna a birnin Landan, kuma ya ci gaba da caccakar sojojin da ke mulki a lokacin da yake gudun hijira.
Gwamnatin Najeriya ta lokacin duk da ba ta huldar jakadanci da kasar Isra’ila, Najeriya ta kasance babar mai samar mata da man fetur, ita kuma tana samar wa Najeriya makamai, kuma hakan ya ba Najeriya damar tuntubar hukumar leken asiri ta Isra’ila (Mossad) don ganowa da dawo da Umaru Dikko Najeriya domin ya fuskanci tuhuma.
A ranar 5 ga Yulin 1984, aka yi yunkurin sato Alhaji Umaru Dikko daga Ingila zuwa Najeriya ta filin jirgin saman Stansted da ke Ingila inda aka iske shi a cikin wani akwati dauke da tambarin ofishin jakadancin Najeriya, wanda hakan ya sa aka zargi Najeriya da hannu a yunkurin sato shi zuwa Legas.
Idan akwai abin da za a ce ya sa marigayi Umaru Dikko yin kaurin suna a Jamhuriyya ta Biyu ga alama bai wuce takaddamar da ya rika yi da wasu manyan mutane da suka hada da Manjo Janar Shehu Musa ’Yar’aduwa da Cif MKO Abiola da Alhaji Umaru Shinkafi da Laftana TY danjuma da Manjo Janar Muhammadu Buhari ba.
 A ta’aziyyar da Mahmud Jega ya yi masa da aka buga a jaridar Daily Trust ta shekaranniya Laraba ya ce:
 “Lokacin da na yi wata tattaunawa da shi a 1988 kan dalilin takaddamarsa da wadannan manyan mutane ya dauki lokaci mai tsawo yana yi mini bayani, inda ya ce takaddamarsa da Shehu ’Yar’aduwa ta faru ne kan batun kirkiro jiha. Dikko ya nemi a raba Jihar Kaduna inda za a ba tsohon Lardin Zariya jiha don samar da sabuwar Jihar Kaduna. Shi kuma ’Yar’aduwa bai son a raba jiharsa. Sannan a lokacin zaben share-fage na dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar NPN yayin da yake yi wa Shagari aikin ’Yar aduwa a matsayinsa na Babban Hafsa a Majalisar koli ta Sojan Najeriya ya goyi bayan Malam Adamu Ciroma, kuma da Adamu Ciroma ya fadi sai ’Yar’aduwa ya daina sha’awar NPN har sai da ta ci zaben Shugaban kasa. Kuma Dikko ya ce lokacin da Shagari ya zama Shugaban kasa sai ’Yar’aduwa ya nemi ya zama Ministan Tsaro da sunan ya taimaka wajen dakile sojoji, Dikko ya ce, sai ya tambaya, “Shin mu awaki ne?  Mun gama aiki sannan ka zo ka debi garabasa.”
Game da takaddamarsa da TY danjuma kuwa, Dikko ya ce, ta faro ne a 1978 lokacin da Babban Hafsan Sojan na lokacin ya yi hasashe ga wasu mutane cewa NPN ba za ta ci zaben 1979 ba. Kuma takaddamar ta dada zafi lokacin da gwamnatin Shagari ta toshe kafafen harkar man fetur na TY danjuma, (a lokacin irin wannan harka ba haramtacciya ba ce). Kuma za ka iya gane fusatar da Dikko ya yi lokacin da Dogarin Janar Buhari, Manjo Mustapha Jokolo daga baya ya fallasa cewa TY danjuma ne ya dauko hayar wadanda suka yi yunkurin sato Dikko daga Ingila a matsayin kwangila daga gwamnatin Buhari da Idiagbon.
Takaddamarsa da Umaru Shinkafi a takaice wanda shi ne Shugaban Hukumar Tsaron kasa (NSO), ita ce ya taimaka wajen juyin mulkin 1983. Shinkafi ya musanta zargin kuma ya kai Dikko kotu. Shinkafi ya kai kara ta lokacin da na ba da rahoton zargin na Dikko a jaridar New Nigerian Weekly, kuma ina fata ba zai sake haka ba.
Akwai abubuwa biyu na tunawa da Dikko ya shaida min a lokacin doguwar tattaunawar. Ya bayyana kansa a matsayin Janar din siyasa, don haka ya kamata sojoji su girmama shi domin shi ma Janar ne a fagensa. Kuma game da zargin da ake yi masa na sace biliyoyin Naira a lokacin da ya jagoranci Kwamitin Shugaban kasa kan shinkafa, Dikko ya dube ni kai-tsaye ya ce: “Dukkan wadannan mutane da suke cewa ina da Dala biliyan biyar a asusuna na banki, Allah Ya karbii addu’arsu.”
Wakilinmu a Kaduna Mohammad Yaba ya ce kanensa Alhaji Lamido Dikko wanda ya tabbatar da rasuwar tsohon Ministan a ranar Talata a Kaduna, ya ce za a kawo gawarsa Najeriya a shekaranjiya Laraba domin yi mata jana’iza.
Ya ce gidan marigayin da ke kusa da ginin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna a Titin Lugard, manyan mutanen da suka yi zamani da marigayin na ta tururuwar zuwa domin yin ta’aziyyar wannan babban rashi.
Ya ce a ta’aziyyar tsohon Gwamanan Jihar Kaduna, Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa ya bayyana marigayin a matsayin dan kishin kasa kuma kwararren dan siyasa da ya ba da gudunmawa wajen tabbatar da dimokuradiyya da hadin kan kasar nan.
Majalisar Gwamnonin Arewa a karkashin Shugabanta Gwamnan Jihar Neja Alhaji Mu’azu Babangida Aliyu ta bayyana rasuwar Alhaji Umaru Dikko a matsayin kalubale ga matasa don su shirya dorawa daga inda mazan jiya irinsa suka tsaya wajen ci gaban kasa da zaman lafiya. Kuma ta bayyana marigayin da dan kishin kasa kuma cikakken dan siyasa da ya sadaukar da kansa domin ci gaban kasa da tabbatar da zaman lafiya, inda ta ce ya bar gibi mai wuyan cikewa.
kungiyar Kare Muradin Arewa (ACF) a ta’aziyyarta dauke da sa hannun Kakakinta Malam Muhammad Ibrahim ta bayyana rasuwar Umaru Dikko a matsayin babban rashi ga Arewa. Ta ce hakika Arewa da Najeriya sun yi babban rashi domin rasuwarsa ta bar gibin da zai yi wuyar cikewa.
Gwamnan Jihar Alhaji Mukhtar Ramalan Yero ta hannun kakakinsa, Ahmed Maiyaki ya nuna alhininsa kan wannan babban rashi, ya ce hakika rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Kaduna musamman yanzu da ake matukar bukatar shawarwarinsa ta yadda za a samar da zaman lafiya da ciyar da jihar gaba.
Marigayi Umaru Dikko ya rasu ya bar matan aure biyu da ’ya’ya 11 da kuma jikoki, za a ci gaba da tuna shi a matsayin dan siyasar da sunansa ya fi tambari a Jamhuriyya ta Biyu.