✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin da yasa Kotun Koli ta dage zaman shari’ar Gwamnoni

Kotun koli ta dage yanke shari’ar jihohin: Kano da Bauchi da Sakkwato da Benuwe. Sai kuma sauran jihohin Imo da Filato. Dalilin da yasa kotun…

Kotun koli ta dage yanke shari’ar jihohin: Kano da Bauchi da Sakkwato da Benuwe. Sai kuma sauran jihohin Imo da Filato.

Dalilin da yasa kotun koli ta dauki matakin dage zaman shari’ar da za a yi yau  Litinin. Sun hada da: Daya daga cikin alkalai bakwai da za su yanke hukuncin ba shi da lafiya.

Ma’aikatan kutun sun ce hukunce-hukuncen da kotun za ta yanke sun yi yawa, kuma wasu hukunce-hukuncen za a yanke ne bayan an saurari lauyoyin bangarorin biyu.

Rahotanni daga kotun na cewa magoya bayan wadanda lamarin ya shafa sun cika kotun makil.

Kotun ta bayyana cewa a gobe Talata za a ci gaba da zaman.