✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin dage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa aka dage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da ake gudanarwa kowace  ranar Larabar a wannan mako, inda…

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin da ya sa aka dage taron Majalisar Zartarwa ta Kasa da ake gudanarwa kowace  ranar Larabar a wannan mako, inda ta ce an yi haka ne don a bai wa sababbin ministoci dama su duba bayanai a kan ma’aikatunsu. Dagewar za ta bai wa ministocin damar shiryawa da gabatar da kiyasin kasafin kudin ma’aikatunsu na shekarar 2020.                                                                                                                                                       A ranar Talatar da ta gabata ne Fadar Shugaban Kasa ta ce ba za a yi taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ba a shekaranjiya Laraba,  saboda a ba ministoci lokaci su karanci takardun ayyukan da suka shafi  ofisoshinsu kafin a rantsar da su. Shugaba Buhari dai ya rantsar da sababbin ministocin ne a ranar 21 ga Agustan da ya gabata.

Kakakin Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana dalilin dage taron, inda ya ce, an dage taron ne don bai wa ministocin da aka rantsar dama su duba bayanan ayyukan da tsofaffin ministoci suka bar musu a ma’aikatunsu.

Hakazalika, an ba su damar ce don su san ma’aikatunsu da kyau ta yadda za su samu damar bayar da gudunmawarsu a tattaunawar da za a yi. “Za su kuma yi amfani da lokacin hutun don shiryawa da gabatar da kiyasin kasafin kudinsu na shekarar 2020,” inji shi.

Idan za a tuna a lokacin rantsarwar Shugaba Buhari ya ce za a rika yin taron Majalisar Zartarwar ce duk mako.