Dalilin dakatar da sakatarorin ilimi da daraktocin lafiya a Bauchi – Gwamnati

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed
Gwamna Bala Mohammed ne mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar a jihar Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta dakatar da Sakatarorin Ilimi da Daraktocin   Lafiya da Ma’ajin kananan hukumomi  20 da ke Jihar Bauchi ne domin  a tabbatar da gaskiya da adalci wajen biyan albashin ma’aikatansu inda ta yi zargin cewa fiye da kashi 40 na ma’aikatan jihar ba su da lambar tantancewa na asusun ajiyarsu ta banki.

Wannan matakin da gwamnatin ta dauka ya jawo ma’aikata dubu 41 da ke jihar ba su karbi albashinsu ba har sai gwamnatin ta kammala bincike. Saboda ta yi umarnin a kebe albashinsu a ajiye har sai an kammala bincike.

Tun a tsohuwar gwamnatin jihar ce ake zargin cewa kudaden da ake biyan albashi a jiha da kananan hukumomi na hauhawa a kowane wata duk da ba a kara yawan ma’aikatan jihar ba.

Wata sanarwa da Kwamishinan Wasta Labarai na Jihar Bauchi Alhaji Ladan Salihu ya fitar, ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin yin bincike da tabbatar da daidaito wajen biyan albashin, kuma Gwamna ya umarci wadanda dakatarwar ta shafa su mika ragamar ayyukansu ga wadanda ke biye da su a wajen aiki.

Gwamnati  ta yi zargin cewa fiye da ma’aikata dubu 41 ne ake biyansu albashi da fansho amma ba su da lambar tantance asusunsu na banki (BBN) wanda hakan ya haura kashi 40 na ma’aikatan jihar. Ma’aikatan da ke aiki a jihar dubu 83 da 885, wadanda ake biya fansho kuma dubu 17 da 314, jimilla dubu 101 da 199.

ADVERTISEMENT

Ma’aikatan da ba su da lambar BBN, a ma’aikatan jiha su 5,316, sashen ilimi na kananan hukumomi mutum 19,605, sannan ma’aikata 1,933 a sashen kula da lafiya a matakin farko na kananan hukumomi, sai masu karbar fansho a jiha su 4,019, wadanda ke karbar fansho a kananan hukumomi kuma 5,870.

Mataimakin Shugaban Kungiyar Kwadago ta Jihar Bauchi Kwamared Dauda Shu’aibu ya roki gwamnati ta janye wannan dakatarwar sannan ya ce yin haka ba tare da tuntubar kungiyar ba na iya kawo rashin fahimta a tsakanin gwamnati da ma’aikata. Ya roki wadanda abin ya shafa su yi hakuri su jira matakin da za a dauka a gaba.

A kokarinta na tabbatar da dakatarwar, gwamnati ta kafa wani kwamiti mai wakilai 17 a karkashin jagorancin tsohon Shugaban Ma’aikata na Jihar Bauchi Sanata Adamu Ibrahim Gumba, domin bincikar dalilin da ya sa ma’aikata dubu 41 ba su da lambar ta BBN, kuma su gano dalilan da ya sa ake biyan su albashi ba tare da lambar ba.

Kuma su gano ma’aikatan gwamnati da jami’an bankuna da ke da hannun wajen aikata wannan laifi, sannan kwamitin ana bukatar ya tantance ma’aikatan da suka cancanta a biya su ya ba gwamnati shawara, an ba kwamitin mako biyu ya kammala aikansa.

Wakilan kwamitin sun hada da tsofafffin shugabannin ma’aikata da shugabannin hukumar ilimi bai-daya da Shugaban Hukumar  Lafiya a matakin farko da jami’an tsaro da shugabannin kungiyoyin kwadago.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya