✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dalilin Gwamnatin Tarayya na samar da rugagen Fulani -Fadar Shugaban kasa

Mai Bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu akwai jihohi guda 12 da suka…

Mai Bai wa Shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu akwai jihohi guda 12 da suka nuna sha’awarsu kan shirin gwamnatin tarayyar na kafa rugagen Fulani makiyaya, da nufin kawo karshen yawace-yawace da dabbobi da Fulanin su ke yi, wanda hakan ke haifar da rikici a wasu lokuta tsakanin su da manoma.

Ya ce, akwai alfanu mai yawa da ke tattare da samar da wuraren kiwon na Fulanin, da suka hadar da samar da ayyukan yi da tsaro ga makiyayan daga masu sace dabbobinsu da kuma damar samar da nagartaccen nama da kuma madarar shanu daga wadannan rugagen.

Sai dai gwamnonin jihohin Kudu maso Gabas, sun yi fatali da tsarin kwata-kwata, suna ma su da’awar cimma wata yarjejeniya da shugabannin Kungiyar Miyetti Allah kan Fulanin su kwashe dabbobinsu daga yankin, sa’annan su zama suna sayan ciyawar kiwo daga yankin Kudu maso Gabas, yayin da su kuma Fulanin za su na sayar mu su da jan nama.