Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Dalilin kafa Kungiyar Rayuwarmu a Yau – Khadija ‘Yar Boss

Khadija ‘Yar Boss da wadansu marayu

Dalilin kafa Kungiyar Rayuwarmu a Yau – Khadija ‘Yar Boss

Mataimakiyar Shugabar Kungiyar Rayuwarmu a Yau ta Kasa (RAYAAS), Khadija Ibrahim ’Yar Boss, ta ce sun kafa kungiyar tasu ce don taimaka wa marayu da gajiyayyu.

Khadija ’Yar Boss, ta ce suna ziyartar asibitoci da gidajen yari don ba da tallafi da cire fursunoni da suke da kananan laifuffuka ta hanyar biya musu tara.

Ta ce ko yara ne suka bata wadanda ba a san garinsu ba suna kokarin yin cigiya idan aka gano garinsu su dauki dawainiyar mayar da su ga iyayensu.

Mataimakiyar Shugabar ta ce a cikin watan azumin da ya wuce sun samu wata yarinya ’yar garin Kankara a Jihar Katsina a Jihar Gombe inda suka mayar da ita wajen iyayenta.

Khadija ’Yar Boss, ta ce yanzu haka suna shirin fara koya wa yara da marayu sana’o’i don samun hanyar dogaro da kai.

Kuma suna tallafa wa almajirai da tabarmin kwana da sauransu don rage musu matsalolin yau da kullum.

Daga nan sai Khadija ta yi kira ga hukumomi su hada karfi da karfe wajen taimaka wa marasa galihu don rage musu radadin zafin rayuwa.