Da Dumi Dumi

Dalilin takaita rigakafin cutar shawara kan ’yan kasa da shekara 45

An takaita rigakafin cutar shawara da aka fara mako biyu da suka gabata ga ’yan wata 9 zuwa shekara 44 ne sakamakon karancin sinadarin rigakafin da Najeriya ta samu zuwa yanzu. Wani babban jami’in lafiya a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da ya bukaci a sakaya sunansa ne ya bayyana haka ga Aminiya a ranar Larabar da ta gabata.

Ya ce daukar matakin ya yi la’akari ne da ’yan kasa da wadannan shekaru saboda sun fada cikin rukunin masu raunin garkuwar jiki idan aka kwatanta su da wadanda suka dara su shekaru.

Jami’in ya ce fara aikin rigakafin ya biyo bayan matakin gaggawa ne da Gwamnatin Tarayya ta dauka don yaki da cutar, bayan gano barkewarta a jihohi 9 da ke kasar nan inda kuma tuni ta kashe mutum 5 a garin Abaji da ke yankin Birnin Tarayyar inda cutar ta fi kamari.

Jami’in ya ce daga cikin alamun cutar akwai fitsari ruwan dorawa sai sauya launin ido, a karshe ta lahanta hanta idan ta yi muni, kuma hakan ke kai ga asarar rai.

Ya ce rigakafin wanda ke tasiri a jikin dan Adam na tsawon shekara 10 bayan yi, yawancin matafiya zuwa kasashen ketare na yin sa a matsayin daya daga cikin ka’idar shiga wata kasa. Haka ya ce rukunin ’yan kasa da shekara 44, su ne yawancin masu yin irin wannan tafiye-tafiyen kuma suna da wannan rigafin a jikinsu.

ADVERTISEMENT

Jami’in ya ce nan gaba kadan kasar nan za ta sake sayo maganin daga kasar Indonesiya inda aka kawo sinadarin rigakafin na yanzu tare da tallafin wasu hukumomin lafiya na duniya. Za a ci gaba da rigakafin cutar wadda ake samunta daga jikin wani nau’in sauro zuwa yau 7 ga Disamba.

Aminiya ta yi wannan bincike ne sakamakon cece-ku-cen da wadansu suka fara yi a kan rigakafin kasancewar an takaita hakan ga ’yan kasa da shekara 44, inda wadansu suka fara zargin cewa shiri ne na kassara haihuwa ga rukunin al’umma masu wannan shekaru kuma a wasu jihohi aka takaita.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya