Search
Subscribe
Dalilin tsige mataimakin gwamnan Kogi Simon Achuba

Dalilin tsige mataimakin gwamnan Kogi Simon Achuba

Majalisar dokokin jihar Kogi ta tsige mataimakin gwamnan jihar Simon Achuba daga mukaminsa.

An tsige Simon daga mukaminsa na mataimakin gwamnan Kogi bayan zarginsa da rashin tafiyar da aikinsa yadda ya kamata tare da tozarta gwamnan jihar Yahaya Bello da kuma jam`iyyarsu ta APC.

Majalisar dokokin jihar Kogin ta yanke shawarar tsige Mista Achuba ne bayan ta karbi wani rahoto daga kwamitin mutum bakwai da babban jojin jihar John Baiyeshea ya kafa, wanda ya gudanar da bincike a kan zargin da ake yi masa. Sannan ya gabatarwa shugaban Majalisar Kolawole Matthew.

Shugaban masu rinjaye na majalisar Abdullahi Bello, mai wakiltar mazabar Ajaokuta, ne ya karanta tuhumar da ake yi wa mataimakin Gwamnan a zauren majalisa, wanda ‘yan majalisa 21 cikin 25 suka amince da tsige Simon Achuba.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin