✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dambarwar zaben fid da ’yan takarar Gwamna a Jihar Ogun

A Jihar Ogun ana ci gaba da samun dambarwar cikin gida a Jam’iyyar APC mai mulki da Jam’iyyar PDP a wajen zaben fid da gwanin…

A Jihar Ogun ana ci gaba da samun dambarwar cikin gida a Jam’iyyar APC mai mulki da Jam’iyyar PDP a wajen zaben fid da gwanin dan takarar gwamna.

Jam’iyyar PDP dai ta kammala zaben fid da gwanin ’yan takarar Gwamna a jihar, inda ta samar da ’yan takara biyu wato Ladi Adebutu, wanda ya fito a bangaren Sikirulai Ogundele da ke shugabantar wani bangare na jam’iyyar; a kuma daya bangaren jam’iyyar da ke biyayya ga Sanata Buruji Kashamu a qarqashin jagorancin shugaban bangaren na jihar, Bayo Dayo sun fitar da dan takarar Gwamnan mai suna Adeleke Shitu.

Bangarorin Jam’iyyar PDP sun gudanar zaben fid da gwanin ne a ranar Lahadin da ta gabata, inda bangaren da suka fitar da Ladi Adebutu suka yi zabensu a dakin karatu na Cif Olusegun Obasanjo, yayin da daya bangaren suka yi nasu zaben a Sakatariyar Jam’iyyar ta Jihar, kuma kowane bangare na tinqahon cewa nasa dan takarar ne na gaskiya.

Sai dai a ranar Talatar da ta gabata Kotun Tarayya da ke Abeokuta ta bai wa Hukumar Zabe ta Qasa  (INEC) da Shugaban Jam’iyyar PDP na Qasa, Uche Secondus umarnin soke zaben da aka yi wa Ladi Adebutu. Hukuncin kotun ya biyo bayan qarar da bangaren Jam’iyyar PDP a qarqashin Injiniya Bayo Dayo ya shigar a gaban kotun.

Ita ma jam’iyya mai mulki ta APC na fama da nata matsalolin a zaben fid da gwani dan takarar Gwamnan, inda aka kai ruwa rana a tsakanin Gwamnan Jihar, Sanata Ibikunle Amosun da wadansu ’ya’yan jam’iyyar da suke adawa da yunqurin        Gwamnan na mara wa Abdulqadir Adekunle Akinlade baya. Tuni dai aka yi ta sanya ranar zaben fid da gwanin ana dagewa.

A ranar Lahadin da ta gabata, mambobin Jam’iyyar APC sun yi dafifi a mazabunsu domin kada quri’a, sai dai sun shafe kusan yini guda ba tare da sun kada quri’ar ba. Wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Ogun, Taiwo Adeoluwa ya fitar kai-tsaye a kafar watsa labarai a jihar, ya yi gargadin cewa kada Shugaban Jam’iyyar APC ta Qasa Adams Oshiomhole ya tayar da qura a jihar, ya ce suna sane da bita-da-qullin da ake shirin yi na qaqaba wa al’ummar jihar dan takarar da ba shi ne zabinsu ba. Don haka ba za su yarda a yi zaben ba har sai an ba su a rubuce, rana da lokacin zaben da kundin tsarin da za a bi a gudanar da shi.