Search
Subscribe
Dan acaba ya fallasa wanda ya kashe matar aure

Dan acaba ya fallasa wanda ya kashe matar aure

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama wani matashi mai shekara 20 mai suna Gbolahan Ismail da ta ce ya yi ikirarin furta cewa ya shiga cikin gidan wata matar aure mai suna Toyin Olobowale ya yi fyade da fashin kudi da yi mata fyade sannan ya kashe ta.

Da yake gabatar da mutanen da ake zargi ga manema labarai a Ibadan, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu, ya ce Gbolahan ya dauki hayar wani dan acaba mai suna Joel Musa ne zuwa gidan marigayiya Toyin da ke rukunin gidaje na Ogidi Akobo a Ibadan inda ya kutsa cikin gidan bayan umartar dan acaba ya jira shi zuwa wani lokaci zai mayar da shi. “A yayin da yake cikin gidan ne ya yi wa matar fyade tare da buga mata karfe a kanta wanda ya yi sanadin mutuwarta nan take,” inji Kwamishinan.

Ya kara da cewa, “Bayan kashe matar da dauke mata kudi da wayar salula, sai Gbolahan ya fito ya tarar da dan acaba Joel, yana jiransa inda ya dauke shi ya koma da shi Unguwar Oju-Irin da ke Akobo a Ibadan.”

Kwamishina Shina Olukolu, ya ce “A yayin da Gbolahan ya mika ladan aiki sai dan acaba ya ga hannunsa jina-jina saboda marigayiyar ta gartsa masa cizo lokacin da yake yi mata fyade. Hakan ne ya sa bayan dan acaba ya sauke wanda ake zargin sai ya koma gidan matar don bincikar abin da ya auku. Kuma isarsa gidan ke da wuya sai ya tarar da mutane suna kururuwar mutuwarta inda bai bata lokaci ya sanar da mutane cewa ya san wanda ya kashe ta sai jama’a suka kama shi suka da mika shi ga ’yan sanda. Kama dan acabar ne ya kai ga kama Gbolahan Ismail da Oyesiji Blessing wanda ya sayi wayar matar daga Gbolahan da Oyekola Mumini da ya yi aikin kawar da sakonni da ke cikin wayar,”  inji Kwamishinan.

A lokacin Gbolahan Ismail yake ganawa da manema labarai cewa, ya yi “Na dade ina kokarin shawo kan matar ta amince da ni amma ta ki ba ni hadin kai. Kuma na je gidanta ne domin kara rokonta amma ban yi niyyar kashe ta a ranar ba.”

Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da mutanen da aka kama da zargin aikata kisan kai da fashi da makami da fyade a gaban kotu domin yanke musu hukunci.

 

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin