Da Dumi Dumi

Dan Arewa: Ba a sonka, ba ka son kanka

“Allah ke son kura ba mutanen gari ba.” Babu shakka Allah ne ke son yankin Arewa amma ba mutanen yankin ko kuma al’umnar kasar baki daya ba.

Tun lokacin da Gwamna Janar Lord Luggard ya hada yankunan Kudancin kasar nan da yankin Arewa kuma matarsa Flora Show ta sanya wa kasar suna Najeriya, yankin Arewa yake ta fama da adawa daga al’umomin sauran yankunan da aka hada su domin zama kasa guda, wato Najeriya.

Da farko an bai wa yankunan iko mai yawa, kuma shugabannin kowane yankin sun yi kokari wajen ciyar da yankunan nasu gaba

 A yankin Arewa ana da Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello a matsayin Firimiya kuma ya yi kokari sosai wajen ciyar da yankin gaba, ta hanyar sarrafa dukiyar da ake samu a wancan lokacin ta hanyar da ta dace. Ganin yadda yake kokari da kuma hangen nesansa ne ya sanya al’ummomin yankin Kudu suka tsorata da shi, domin shi kansa Shugaban yankin kasar Yarbawa marigayi Obafemi Awolowo ya taba bayyana Ahmadu Bello da cewa “Mutum ne mai hangen nesa kwarai da yake yin shiri domin abin da zai zo bayan shekara dubu.”

ADVERTISEMENT

Amma duk da kokari da himmar da marigayi Ahmadu Bello ya nuna sai da ya yi ta fama da adawa mai zafi daga bangaren mutanensa na Arewa, ya sha fama da ’yan hana ruwa-gudu. An ruwaito cewa saboda matsin lambar da yake samu ne ya sanya dole ya bar halartar Sallar Juma’a a Masallacin Titin Kano da ke garin Kaduna ya rika zuwa Rigachikum, daga baya ya gina masallacin Sultan Bello a kusa da gidansa da ke Unguwar Sarki a Kaduna ya rika Sallar Juma’a. Haka kuma akwai lokacin da ’yan zanga-zanga suka tare ayarinsa, amma da ya tsaya ya fito daga mota domin ya ji korafinsu sai suka watse. Haka nan dai ya yi ta fama da adawa daga ciki da wajen Arewa har sai da ta kai an kashe shi a wani yunkurin juyin mulkin da sojoji ’yan kabilar Ibo suka shirya a ranar 15 ga watan Janairun 1966.

Bayan wannan gwarzon shugaba ya fadi sai soja suka kwace mulki, Aguyi Ironsi wani dan kabilar Ibo ya zama Shugaban kasa, amma sai sojoji ’yan Arewa suka yunkura suka kwace mulki daga hannunsa, inda aka nada Yakubu Gowon dan yankin Arewa a matsayin Shugaban kasa, daga bisani aka kirkiro da jihoji 12, inda yankin Arewa yake da jihohi 6 yankin Kudu kuma yake da 6, amma duk haka dai an ci gaba da kallon yankin Arewa a matsayin dunkulalle. 

Bayan Yakubu Gowon ya kwashe shekara 9 a mulkin Najeriya sai aka kifar da gwamnatinsa inda marigayi Murtala Muhammad ya zama Shugaban kasa a 1975. Wannan juyin mulkin ya kara farraka yankin Arewa, domin kabilun da Janar Gowon ya fito daga cikinsu suna ganin ba a kyauta masu ba, tunda aka sauke dansu daga mulki, saboda  haka a ranar 13 ga watan Fabrairu sojojin da suka fito daga yankin da Gowon yake a karkashin jagorancin Kanar Dimka suka  kashe  Murtala a daidai lokacin da shi ma ya kama hanyar inganta kasar nan ta yadda yankin Arewa zai amfana. Domin shi ne ya canja hedkwatar kasar nan daga Legas zuwa Abuja, wadda da Legas ta ci gaba da zama hedkwatar kasar nan da al’ummar Arewa sai dai su zama ’yan kallo a kasar nan, domin mutum yana ji yana gani zai bar hakkinsa saboda ba zai iya zuwa Legas ba, ko kuma ba zai iya zama a Legas ba.

Haka dai aka yi ta samun shugabanni daga yankin Arewacin kasar nan suna zama shugabannin kasa amma da taimakon ’yan uwansu ’yan Arewa ake ganin bayansu, saboda ba a so a ce sun yi abin kirki.

Al’ummar Kudu idan sun ga wani Shugaba daga yankin Arewa zai yi abin kirki sai su sanya shi a gaba da suka ta adawa, su matsa masa, amma maimakon mutanen Arewa su yi nazarin dalilin matsa masa da ’yan Kudun ke yi, sai su bi nasu su ma su shiga cikinsu suna matsa masa har sun kai shi kasa, sannan daga baya sai su rika shirya tarurruka suna cizon yatsa suna kuma yabonsa.

Al’ummar Arewa sun zama kamar ’yan amshin shata ga al’ummar Kudu, da zarar ’yan Kudu sun fara sukar wani abu da zai amfani Arewa maimakon ’yan Arewa su taimaka wajen kare shugaban sai kawai su biye wa ’yan Kudun wajen sukar, abin  misali shi ne wata cibiyar horar da manyan jami’an harkar man fetur da marigayi Umaru ’Yar’aduwa ya so budewa a Kaduna, amma ’yan Kudu suka taso da sukar batun suna cewa don me za a bude irin wannan cibiyar a yankin da ba a hakar mai, alhali ba ma’aikatar hakar mai za a horar a cibiyar ba, cibiya ce ta horar da manyan jami’ai kwatankwacin irin wadda ake da ita a Kuru kusa da Jos domin horar da manyan jami’an gwamnati. Yanzu haka wurin na nan an bar shi sai manyan gine-gine, an yi watsi da aikin, kuma cikin masu sukar gina cibiyar har da ’yan Arewa.

Wani abu da ya faru kwanan nan shi ne korar Babban Daraktan Hukumar Tsaro ta DSS Lawal Daura da Mukaddashin Shugaban kasa Osinbajo ya yi a lokacin da Shugaba Buhari ke hutu, saboda dan Arewa ne aka cire kuma aka maye gurbinsa da dan Kudu, sai ’yan Kudu suka yi ta yabawa, su ma ’yan Arewa haka suka yi ta tafi, alhali kamata ya yi tunda ana zargin Lawal Daura da aikata ba daidai ba ne sai a dakatar da shi a gudanar da bincike, idan laifinsa ya tabbata sai a cire shi, amma ba a yi haka ba, kuma ba a so a ji bangarensa. A yanzu kuma ’yan Kudu sai cewa suke ba su yarda a karbe shugabancin hukumar daga hannun Mathew Seiyefa wanda aka ba riko ba, duk da cewa dama wata uku suka rage masa ya yi ritaya daga aiki.

Kuma wanda Lawal Daura ya gada Ita Ekpenyong an nada shi ne a watan Satumban shekarar 2010 aka sauke shi a watan Yulin shekarar 2015, amma saboda dan Kudu ne babu wanda ya yi surutu a zamaninsa duk da abubuwan da suka yi ta faruwa.

Haka ake ta yi a zamanin mulkin Goodluck Jonathan, sai jaridun Kudu sun sanya wani dan Arewa a gaba nan da nan sai ka ji an bayar da sanarwar sauke shi kuma a maye gurbinsa da dan Kudu, kuma saukewar ta wulakanci ake yi. Misali an sauke Shugaban Sojin kasa Janar Abdurrahman Dambazau yayin da yake kasar Amurka yana halartar wani taro, an sauke Gwamnan Babban Banki Sanusi Lamido Sunusi (Sarkin Kano na yanzu) yana wajen taro a kasar Nijar, an sauke Shugaban ’Yan sanda, Suleiman Abba yana ofis yana ta aiki bai san an sauke shi ba. Haka dai ake ta yi wa manyan Arewa wulakanci ana sauke su daga mukamansu ana maye gurbinsu da ’yan Kudu. 

An dade ana ta kururuwar sai an sauke manyan hafsoshin sojan sama da na kasa masu ci a halin yanzu saboda ’yan Arewa ne.

Don Lawal Daura ya fito daga gari daya da Shugaba Buhari ba zai hana a yi masa adalci ba, domin shi ma dan Najeriya ne.

Ya kamata ’yan Arewa su hada kansu idan ba haka ba, za a yi musu sakiyar da babu ruwa saboda sakacinsu. Yanzu ga shi zabe ya karato amma ’yan takarar Shugabancin kasar nan daga yankin Arewa sai karuwa suke yi, kuma kowanne so yake dole sai shi, idan dai suka yi sakaci za su ji ta a salansa, domin ’yan Kudu za su iya mara wa nasu baya ya zama Shugaban kasa, sai dai a bar ’yan Arewa da tafa hannu.

dan Arewa ne kawai ya yarda cewa dan kowane yanki dan Najeriya ne, amna ’yan Kudu suna ganin  dan Arewa a matsayin kaska ne rabi mai jini. Don haka tun da wuri ya kamata ’yan Arewa su farka su rika kaunar junansu, maimakon kware wa ’yan uwansu baya, domin taimakon Allah ne ya sanya har yanzu ake da yankin Arewa, amma da domin mutanen cikinsa ne da tuni yankin ya dade da wargajewa, sai dai tarihi, don ana ta kokarin wargaza yankin a ciki da wajensa, saboda mutanen yankin sun kasance ba a sonsu kuma ba su son kansu. Arewa dai ita ce Najeriya. Da sauran yankunan kasar nan ne suke da yawan mutane irin na Arewa to idan suka rike mulki sai mahadi, ba za su taba yarda da tsarin karba-karba ba

Marigayi Malam Aminu Kano dai yana cewa, “Najeriya daya ce, amma kowa ya san gidan ubansa.” Ba laifi ba ne idan ka ga za a cuci dan uwanka ka taimaka masa, amma idan aka kawar da kai ka bari aka zalunce shi ba ka kyauta ba kuma za ka yi da-na-sani.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya