Daily Trust Aminiya - Dan banga da masu satar mutane 3  sun yi mutuwar kasko a Ada
Subscribe

Sufeto Janar Adamu Muhammad

Dan banga da masu satar mutane 3  sun yi mutuwar kasko a Adamawa

Wani dan banga mai rike da sarautar Kaigaman Nyibango, Alhaji Haruna Gamjango ya yi mutuwar kasko da wadansu da ake zargin masu garkuwa da mutane su uku wadanda suka kai masa hari a gidansa da ke Unguwar Jarandi – a Mayo Ine da ke Karamar Hukumar Jada a Jihar Adamawa.

Wani wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce wadanda ake zargin sun shigo gidan Alhaji Haruna da misalin karfe 11 na dare ne ranar Litinin da ta gabata inda suka yi kokarin yin garkuwa da shi.

“Sun kwankwansa kofarsa da ya bude sai suka yi kokarin tafiya da shi, har da harbinsa amma harbin bai yi tasiri ba. A nan ne suka fara fada a tsakaninsu. Ya harbi uku daga cikinsu, mutum daya ya mutu nan take.

“Kasancewar sarkin yawa ya fi sarkin karfi, sai suka fi karfinsa suka kashe shi,” inji majiyar. “Sauran biyu ma da ya harba sun mutu daga baya inda aka kai gawawaki hudun zuwa ofishin ’yan sanda na Jamtiri inda ake gudanar da bincike kan lamarin,” inji shi.

Wani da muka zanta da shi da aka sakaya sunansa ya ce daya daga cikin masu garkuwan da ya mutu, mazaunin unguwar ne kuma ana zarginsa da yin garkuwa da mutane.

“An sako shi wata uku da suka gabata kuma ga shi ya sake komawa aikata garkuwa da mutane,” inji shi.

Da aka tuntuvi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Adamawa DSP Suleiman Nguroji kan lamarin, ba a same shi ba sannan da aka turo masa sakon tes har hada wannan rahoto bai amsa ba.

Garkuwa da mutane a Jihar Adamawa ta zama babbar matsalar  da take addabar jama’a.

texem
More Stories