✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan dambe Ebola na fuskantar shari’a a kan naushe wata budurwa

Wani dan damben gargaijya Abdurrazak Ahmed wanda aka fi sani da Ebola na fuskantar shari’a a gaban Kotun Majistare da ke GRA, Chediya a Zariya…

Wani dan damben gargaijya Abdurrazak Ahmed wanda aka fi sani da Ebola na fuskantar shari’a a gaban Kotun Majistare da ke GRA, Chediya a Zariya bisa zarginsa da doke wata budurwa mai suna Farida Muhammed inda ta suma na tsawon lokaci kafin ta farfado wanda hakan ya saba wa sashi na 224 na Final Kod.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 23 ga Maris, 2019 da misalin karfe tara na dare kamar yadda bayanan farko na bincike ’yan sanda ya nuna.

Bayan an karanta wa shahararren dan damben Abdulrazak Ebola tuhumar da ake masa sai ya ki amaicewa ya aikata laifin inda lauyansa Gabriel A. Attah ya nemi da kotu ta bayar da belinsa, amma mai gabatar da kara Saje Mannir Nasir ya ki amincewa da bukatar lauyan bisa hujjar cewa wanda ake zargin zai iya yin katsalanda ga bincike ’yan sanda. Haka kotun ta ki bayar da belin tare da kai shi gidan yari don zaman jiran shari’a. Bayan da suka bayyana a ranar Talata don ci gaba da shar’ar sai dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana wa kotu cewar dukkan bangarorin biyu suna kotu kuma a shirye suke don ci gaba da shari’ar.

Dan sanda mai gabatar da kara Saje Mannir Nasir ya gabatar da shaidarsu ta farko wato dan sandan da ya gudanar da bincike mai suna Saje Adamu Adams inda ya yi wa kotu bayanin abin da ya faru.

Babban  Majistare Abubakar Aliyu Lamido ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar Laraba 17 ga Afrilu kuma kotun ta bayar da belin dan dambe Abdulrazak Ebola a kan Naira miliyan daya tare da wanda zai tsaya masa a kan Naira dubu 500.