Dan Iyan Zazzau Alhaji Yusuf Ladan ya rasu

Allah Ya yi wa Alhaji Yusuf Ladan, Dan Iyan Zazzau rasuwa bayan fama da rashin lafiya.

Alhaji Yusuf Ladan ya rasu a gidansa da ke Kaduna safiyar Talata, 10 ga watan Nuwamba, 2020 yana da shekara 86 a duniya.

Za a yi sallar jana’izarsa bayan sallar Azahar a Masallacin Juma’a na Maiduguri Road, Kaduna.

A lokacin rayuwarsa, Marigayi Alhaji Yusuf Ladan ya kasance fitaccen dan jarida, tsohon Manajan

Daraktan Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin na Jihar Kaduna (KSMC), kuma Hakimin Kabala.