Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dan kasar Togo ya nemi ’yan sandan Najeriya su kamo mutumin da ya sare masa hannu

Adamu Issa a gadonsa na asibiti
Adamu Issa a gadonsa na asibiti

Wani manomi dan kasar Togo mai suna Adamu Issa da ya saba shigowa Najeriya a kowace shekara domin noma abin da zai ci da iyalinsa ya yi kira ga ’yan sandan Najeriya su taimaka wajen gano mutumin da ya sare masa  hannu lokacin wani sabani a cikin gonarsa a kauyen Bolorunduro da ke Karamar Hukumar Orire a Jihar Oyo.

Adamu Issa ya yi wannan kira ne lokacin da yake yi wa manema bayani a gadonsa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar LAUTECH da ke Ogbomoso, inda ake yi masa jinyar munanan raunukan da ya samu a sassan jikinsa. Ya ce, “A kowace shekara lokacin damina ina tasowa tare da iyalina daga kasar Togo zuwa kauyen Bolorunduro inda nake noma kayan abinci musamman rogo da ina sayarwa in samu abui da za mu ci da iyalina tare da samun kudin da muke rikewa a hannu mu koma kasarmu (Togo).  Amma a bana na shigo Najeriya da kafar hagu domin ka gane wa idonka halin da nake ciki a gadon asibiti. Shi ne ya sa nake kira ga ’yan sanda su taimaka su gano mutumin da ya same ni a cikin gona ya sa adda ya sare mini hannu ya tsere. Mutumin ya yi nufin hallaka ni ne ta hanyar kai min sara da adda a wuya amma sai na sanya hannu domin kare kaina wanda ya yi sanadin guntile hannun nawa nan take,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Ya kara da cewa: “Ina so jami’an tsaro su kamo mutumin su yi binciken gaskiyar a lamarin domin yin adalci. Ina so mahukunta su tilasta mutumin ya biya diyya gare ni kuma a tilasta masa biyan kudin asibiti da barnar kayan abincin gonata da dabbobinsa suka yi.”

Adamu Issa, ya ce “Mutumin ya koro shanunsa cikin gonata ce a lokacin da nake noma inda na shawarce shi ya karkatar da dabbobin zuwa gefen gonar amma abin mamaki sai ya wuce a fusace ya je ya dawo ta bayana ya kama sarana  da adda ya gudu ya bar ni kwance jina-jina a gonar. Matata mai suna Gbera da dana Amidu ne suka fara kawo min dauki inda suka garzaya suka sanar da al’ummar kauye suka dauke ni zuwa babban ofishin ’yan sanda na Ikoyi. Abin bakin ciki shi ne har yanzu ba a iya kama  mutumin ba.”

ADVERTISEMENT
 Hannunsa da aka guntule
Hannunsa da aka guntule

Dagacin kauyen Bolorunduro Cif Oyedokun Adeboye, ya ce duk da yake har yanzu ba a kama mutumin da ya aikata wannan danyen aiki ba, amma ya kamata shugabannin Fulani makiyaa a yanki su dauki nauyin biyan kudin asibiti da kudin diyya da Adamu Issa zai yi amfani da su wajen rikewa a hannu ya koma kasarsu domin sake sabuwar rayuwa.

Kakakin Runduar ’Yan sandan Jihar Oyo SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce yanzu haka Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Shina Olukolu, ya mika al’amarin ga Sashin Binciken Manyan Laifuffuka (CID) domin kamo mutumin da ya aikata wannan danyen aiki don hukunta shi. Kakakin ’yan sandan ya musanta zargin da al’ummar kauyen Bolorunduro suka yi cewa, ’yan sanda sun ki daukar mataki tun lokacin da al’amarin ya auku, inda ya ce bai kamata a rika yi musu irin wannan zargi a daidai lokacin da suke bincike don gano maboyar mutumin ba.