Da Dumi Dumi

Dan kishin kasa Bukar Usman Biu (2)

Dokta Bukar Usman ne a hagu, yana amsar kambin karramawa daga hannun Shugaban Jami’ar Najeriya Nsukka, Farfesa B. C. Ozumba a shekarar 2016
Dokta Bukar Usman ne a hagu, yana amsar kambin karramawa daga hannun Shugaban Jami’ar Najeriya Nsukka, Farfesa B. C. Ozumba a shekarar 2016

Najeriya kasarmu ta gado, Najeriya Babbar Kasa! Kasar da masu kishinta ke tinkaho da ita, a yayin da wadansu ke hankoron durkusar da ita. Kasar da wadansu tuni suke ambaci cewa ta durkushe, inda har ma aka samu wani marubuci mai suna Chinua Achebe ya yi jana’izarta a littafinsa mai taken: Nigeria: There was a Country. Kasar da kuma a hannu daya ke dauke da muzakkaran masu kishinta da suke cikin yi mata hidima, ba ji ba gani. Dan jarida kuma marubuci, OWEI LAKEMFA ya tsamo irin wadannan mutane da ke raye a yanzu, mai suna Dokta Bukar Usman Biu, OON, ya rubuta mukalar nan game da shi, da nufin karfafa masa gwiwa a wani bangaren kuma ya kara wa sauran ’yan kishin kasa kaimi. Ganin muhimmancin mukalar ya sa GIZAGO (08065576011) ya fassara daga Ingilishi zuwa Hausa. Mun kawo kashi na daya makon jiya, yau ga karashe:

Na cika da mamaki a lokacin da na ga wayata tana kadawa kuma da na duba sai na ga Dokta Usman ne ya kira ni. Ya bukaci in gaya masa adireshin ofishina, domin zai aiko mini da wasu littattafai, musamman dama ya yi tsammanin ina kaunar littattafai. Ko kadan ban yi tsammanin zai aiko mini shirgin littattafai kamar wadannan ba: Kunshi ne mai girma, dauke da littattafai, mujallu da ingantattun kananan takardu. Littattafai ne da aka wallafa da inganci, kunshe da dimbin ilimi, ba wai irin littattafan nan na je-ka-na-yi-ka ba, wadanda wadansu tsofaffin manyan ma’aikata kan rubuta cike da bambadanci.

Cikin littattafan nan har da wani dirkeke da aka wallafa a Oktoban 2014, mai suna: Tarihin Biu. Littafi ne da ya amsa sunansa, kammalalle kuma ingantacce mai dauke da shafuka 693, wanda aka rubuta a kan tarihin garin Biu, hedikwatar al’ummar Babur/Bura, garin da ya zama masarauta a 1535. Haka kuma a cikin kunshin akwai littattafan yara masu dauke da gajerun kirkirarrun labarai da tatsuniyoyi.

Na kara tsinkewa da al’amarin Dokta Bukar. Idan ka debe Obasanjo, a iya sanina ban san wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ya kasance mai amfanar al’umma da iliminsa ba. Amma yanzu na kara samun wani muzakkari, wanda har ma ya fi Obasanjo amfanar da al’umma a janibin ilimantarwa, domin kuwa shi littattafansa sun karade kowane fagage da suka hada da siyasa, tarihi, al’ada da kuma adabi. A watan Yulin nan da ya gabata ma sai da Dokta Usman ya sake aiko mini da kyautar wasu sababbin littattafan nasa har guda takwas, wadanda suka danganci ilimin gudanar da al’amuran gwamnati da harkar tsaro. Daya daga cikin littattafan, an wallafa shi ne a shekarar 2018, wanda kuma yake kunshe da tarihin rayuwarsa. Littafi ne mai dauke da shafuka 287 mai taken “Cikar Buri” wanda kamfanin wallafa na Bookraft ya wallafa.

Bayan na yi ninkaya a kogin littattafansa, sai na fahimci cewa Bukar masani ne na gaske, mai yi wa al’umma hidima, wanda yake da kokarin adana tarihinmu da killacewa tare da tsefe al’adunmu, wanda ke hakilon hidima da nufin gina ingantaccen aiki domin amfanin al’ummar yanzu da masu zuwa nan gaba. Yana haka ne ba domin amfanar da kansa ba, sai domin Najeriya. A yanzu haka shekararsa 77 a duniya, masani mai saukin hali, mai tafiyar da rayuwarsa cikin tsari domin jin dadin al’ummar kasa.

ADVERTISEMENT

Kasar China na da wata muhimmiyar al’ada, wacce ta sanya ta bunkasa. Wannan al’ada ita ce yadda take gina kasarta ta amfani da tsofaffin al’adun mutanenta na dauri da suka gabata. Haka shi ma Dokta Bukar, yana da irin wannan dabi’a da yake amfani da ita domin gina Najeriya. Domin cimma wannan manufa, ya sadaukar da dukiya mai yawa da lokacinsa, ya tattara da sake rubuta tatsuniyoyi, hikayoyi da hikimomin al’ummar kasar nan na dauri, domin al’ummarmu na yanzu da masu zuwa su ci gajiyarsu wajen gina kasa. A nazarin da na yi, na fahimci cewa babbar gudunmawar da Bukar ya ba mu ta hada da wasu littattafai guda biyu, wadanda ke kunshe da bayanan asalinmu da al’adunmu. Littafi na farko, yana kunshe ne da zababbun tatsuniyoyi, wadanda ke dauke da ma’anonin rayuwa da al’adar mutanenmu na dauri. Littafin yana dauke da shafuka 787, wanda a cikinsa akwai hikayoyi 700 daban-daban, wadanda suka hada da hikayoyin da suka shafi masunci, dukiya, abokantaka, jarumta, tsafi, maharbi, tarbiyya, fadar sarki, mai sihiri, yaki, aure da kuma hikayar wata tsohuwa.

Littafi na biyu wanda ke kunshe da hikayoyin da suka shafi mutane, dabbobi, aljanu da kuma abubuwa, yana dauke da shafuka 939, wanda a cikinsa akwai hikayoyin al’ummun Najeriya har guda dubu daya. Kuma duk an wallafa su ne a karkashin tsarin littattafansa na TNT (The Treasury of Nigerian Tales) – Rumbun Hikayoyin Najeriya). Kuma ya sadaukar da su ga “dukkan mutanen da ke kokarin tallafi da rainon tatsuniya, wacce ita ce makarantar farko ga yara.”

Kamar yadda ya bayyana, Bukar ya ce manufarsa ta wannan aiki na TNT ita ce: “Domin tattara hikayoyi da tatsuniyoyi da killace su da adana su, domin kuwa irin wadannan hikimomi na mutanen dauri suna bacewa. Wannan aiki kuma burina ne a bunkasa alaka da zumunta tsakanin al’ummomi masu mabambantan al’adu, wanda haka zai jaddada zumunci da girmama al’adun juna. Hikayoyi ne da na tattaro daga karkara, aka wallafa su domin ilimantarwa, nishadantarwa, sannan kuma domin su karfafa wa matasa wajen koyon tarbiyya da dabi’u kyawawa domin ci gaban al’umma gaba daya.”

A kokarinsa na tabbatar da dorewar Najeriya, da raba ta da barazanar kabilanci da nuna bambancin addini da kitimirmirar ’yan boko masu hadama, Bukar ya maida hankalinsa kacokan wajen samar da littattafai ga al’umma. Ya yi ritaya daga aiki a 1999, ya rubuta littattafai 20 a cikin shekara bakwai, sannan yana ci gaba da kokarin samar da wasu. Bukar Usman ya biyo sahun marubuta irin Farfesa Wole Soyinka da Odia Ofeimun – marubutan da ba su yi kasa a gwiwa ba, duk da irin matsanancin yanayin da Najeriya ta samu kanta a ciki na matsalolin siyasa da sauransu, suka ci gaba da ba ta ruwa ta hanyar samar da littattafan ilimi da ake kishirwarsu.

Najeriya kasa ce mai wuyar sha’ani, wacce za ta iya dugunzuma ka ba da shiri ba, amma duk da haka ina alfahari da muhimman mutane masu kishin kasa kamar Dokta Bukar Usman da Udenta Onwuamaeze Udenta, wanda a yanzu haka yana da littattafai 21 da ke kan hanya daga kamfanin wallafa na Kraftbooks. Haka shi ma Odia Ofeimun, wanda a duk lokacin da gardama ta hada shi da mutum zai zaro littafin da ya rubuta a kan mas’alar. Odia a yanzu haka yana shirin fitar da littattafai 40 a badi, ranar 16 ga Maris, a daidai ranar da zai cika shekara 70 a duniya. Muna da irin wadannan zaratan masana masu fikira, wane ne zai yi mana gori, ya ce Najeriya ba ta da albarka?

Mun kammala

Share