Da Dumi Dumi

Dan kishin kasa Bukar Usman Biu

Daga dama, Dokta Bukar Usman ne, yayin karrama shi a Bikin Tunawa da Abubakar Imam a Kaduna, a shekarar 2017
Daga dama, Dokta Bukar Usman ne, yayin karrama shi a Bikin Tunawa da Abubakar Imam a Kaduna, a shekarar 2017

Najeriya kasarmu ta gado, Najeriya babbar kasa! Kasar da masu kishinta ke tinkaho da ita, a yayin da wadansu ke hankoron durkusar da ita. Kasar da wadansu tuni suke ambata da ta durkushe, inda har ma aka samu wani marubuci mai suna Chinua Achebe ya yi jana’izarta a littafinsa mai taken: ‘Nigeria: There was a Country.” Kasar da kuma a hannu daya ke dauke da muzakkaran masu kishinta da suke cikin yi mata hidima, ba ji ba gani. Dan jarida kuma marubuci, OWEI LAKEMFA ya tsamo irin wadannan mutane da ke raye a yanzu, mai suna Dokta Bukar Usman Biu OON, ya rubuta mukalar nan game da shi da nufin karfafa masa gwiwa a wani bangaren kuma ya kara wa sauran ’yan kishin kasa kaimi. Ganin muhimmancin mukalar ya sa GIZAGO (08065576011) ya fassara daga Ingilishi zuwa Hausa:

Kasar Amurka ta kware wajen kitsa giri da handama da babakere, ta yi zarra wajen haddasa yake-yake iri-iri, har ma ta shahara wajen mallakar miyagun makamai na kare-dangi da na nukiliya. Kasar kuma tana bugun kirji da shahararrun masana kimiyya na duniya. Wannan kasa ta Amurka ta dade tana bibiyar Najeriya, ta jima tana yi mata kallon kurulla. Ta yi ta zakulo gazawarta da cutttukanta da matsalolinta, inda a karshe ma ta bayyana cewa laulayin Najeriya ba zai warke ba, kasar gab take da zuwa kushewa.

Amurka ba ta tsaya nan ba, ta yi ta ba da shawarar cewa lallai ya kamata a dora Najeriya a gadon jinya, a daura mata iskar oksijin, kafin ta ida mutuwa. Hukumar Leken Asiri ta Amurka (CIA) ta fitar da wani rahoto nata a cikin watan Maris na 2005 mai taken: “Sake Fasalin Taswirar Duniya,” inda a ciki ta bayyana da babbar murya cewa Najeriya a yadda take, “aure ne marar inganci,” wanda zai warware a shekarar 2015.

A nan, rahoton na nufin cewa yadda aka harhada yankunan Najeriya masu dauke da mabambantan kabilu zuwa kasa daya a 1914, tamkar aure ne da ba zai dore ba. A ganin Amurka, Najeriya ta yi karko da har ta ci gaba da dorewa a matsayin kasa daya, duk da cewa tana kunshe da gamin-gambizar kabilu da harsuna da addinai da al’adu mabambanta.

Haka kuma, a cikin watan Maris na shekarar 2010, tsohon Shugaban Libya, marigayi Mu’ammar Ghaddafi ya taba yin nazarin Najeriya, inda a karshe ya bayyana cewa matukar kasar na son dorewa, to babu makawa sai an raba ta zuwa gida biyu ta fuskar addini, idan ba haka ba kuwa to abin da zai faru da ita zai yi kama da girgizar kasa mai tsananin muni.

ADVERTISEMENT

Wannan tunani na Amurka da na mutane kamar su marigayi Ghaddafi da marubuta irin su marigayi Chinua Achebe da ma sauran wadanda ba mu ambata a nan ba, wadanda ke ganin cewa Najeriya ba za ta dore ba a matsayin kasa daya, a gefe guda akwai zakakuran mutane da suke aiki ba dare ba rana wajen yi wa Najeriya hidima, wadanda suke da yakinin cewa kasancewarta a matsayin dunkulallar kasa mai ’yanci, abu ne mai yiwuwa kuma za ta ci gaba da dorewa har ila masha Allahu.

Ni kaina, na san da wani muzakkari, halattaccen dan Najeriya, Dokta Bukar Usman Biu, OON daga Jihar Borno, wanda yake da yakini game da dorewar Najeriya. Mutumin nan ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi mata hidima, domin ganin dorewarta har gaba da gaba can mai nisa.

Na taba ganawa da shi a shekarar 2016, inda muka dan tattauna kan al’amura daban-daban a gurguje. A lokacin, na hadu da shi ne a Abuja, yayin wani taron lacca da Kungiyar Wayar Da Kan Al’umma Dangane Da Al’amuran Kasa-Da-Kasa (SIRA) ke gabatarwa shekara-shekara. A yayin da na gamu da shi muka fara tattaunawa, na yi ta kawo wa raina inda na taba haduwa da shi, domin kuwa ba wannan ne karon farko da na taba ganin fuskarsa ba, amma dai na mance.

Bayan an kammala wannan taro da muka halarta, mahalarta na musabaha da juna, ana yin ban-kwana, sai Dokta Bukar ya bukaci in ba shi lambar wayata. A cikin hikima da azanci, sai na nuna masa cewa na kasa tunowa da sunansa.

“Bukar Usman,” ya fada mini cikin murya mai cike da azanci. Nan take ni kuma sai na yi firgigi, kamar na tsorata. Shi kuma ya ankara da wannan yanayi da na shiga, kawai sai ya yi murmushi. Ya kara tambayata cewa ko zan ba shi lambar?

Ga ire-irenmu ’yan gaba-dai-gaba-dai, wadanda suka yi kaurin suna wajen adawa da mulkin soja, sunansa a rubuce yake a kwakwalwarmu, kasancewarsa masani a harkar tsaro. Ya yi suna wajen kwarewarsa a nazarin al’amuran tsaro, duk da cewa ba a cika ganinsa a fili ba, aikinsa na karkashin kasa da suka hada da rubuce-rubuce da mukaloli da suka shafi tsaro sun yi fice.

Kwakwalwata ta yi ta nazari, inda a cikin kankanen lokaci na tuno cewa na taba haduwa da shi a 1990. A lokacin nan ba a dade da bankado shirin ‘Juyin Mulkin Orkar’ ba. Na kasance daya daga cikin ’yan jarida da Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya ta wakilta domin ganawa da Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, Birgediya Janar Haliru Akilu da nufin bukatar a sako ’yan jaridar da aka tsare. Na tuno sosai da wannan lokacin, yau shekara 26 ke nan da ta gabata, ga shi a yanzu na sake haduwa da Bukar Usman a karo na biyu.

Bayan na tunano wannan al’amari sai nan da nan na dawo cikin hayyacina, na ba shi lambar wayata da ya bukata. Ya shaida mini cewa ya yi ritaya, bayan ya shafe shekara 35 a hidimar kasa, inda cikin wadannan shekaru, ya kwashe shekara 27 a Ofishin Zartarwa na Gwamnatin Tarayya. Ya yi aiki tare da shahararrun mutane kamar su S.B. Agodo, Babagana Kingibe, Umaru Shinkafi, Isma’ila Gwarzo, A.K. Horsfall, Janar Abdullahi Mohammed, Janar M.C. Ali da Janar I.D. Gumel.

Za mu kammala makon gobe

 

Share