✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Aljeriya Baghdad ne ya fi yawan zura kwallaye a 2018

Rahotannin da ke fiowa sun ce dan kwallon Aljeriya Baghdad Bounedjah ne ya fi kowane dan kwallo yawan zura kwallaye a raga a shekarar 2018…

Rahotannin da ke fiowa sun ce dan kwallon Aljeriya Baghdad Bounedjah ne ya fi kowane dan kwallo yawan zura kwallaye a raga a shekarar 2018 a fadin duniya.

Dan kwallon ya shiga gaban Lionel Messi, dan kwallon FC Barcelona da Cristiano Ronaldo, dan kwallon Jubentus.

Baghdad ya zura kwallaye 59 ne a raga a 2018 yayin da Lionel Messi ya zura kwallaye 51 Cristiano Ronaldo kuma ya zura kwallaye 49.

Baghdad yana buga wa kulob din Al-Sadd na Katar wasa ne, kuma a wani wasa da ya yi a gasar rukuni-rukuni na Katar ya taba zura kwallaye bakwai a wasa daya, a wasan da kulob dinsa ya doke na Al-Arabi da ci 10-1.

Sai dai dan kwallon bai ja hankalin duniya ba ne saboda yana wasa ne a yankin Asiya.  Masana harkar kwallo suna ganin da yana wasa ne a Nahiyar Turai da kafofin watsa labarai sun fi yayata shi.