✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Arsenal Podolski zai shafe mako uku yana jinya

Shahararren dan kwallon gaba a kulob din Arsenal da ke Ingila Lukas Podolski ya samu matsala a jijiyoyin cinyarsa a wasan da kulob din ya…

Lucas PodolskiShahararren dan kwallon gaba a kulob din Arsenal da ke Ingila Lukas Podolski ya samu matsala a jijiyoyin cinyarsa a wasan da kulob din ya yi da na Fenerbache a ranar Talatar da ta gabata na neman hayewa gurbin gasar cin kofin zakarun kulob-kulob na Nahiyar Turai (UEFA Champions League).
A wasan, kulob din Arsenal ya doke na Fenerbache ne da ci 2-0, sannan a wasa zagaye na farko da aka buga a gidan Fernebache a makon jiya, Arsenal ta lallasa ta ne da ci 3-0.  Kenan idan aka hada wasannin biyu, Arsenal ce ta samu nasara da ci 5-0.
Kocin Arsenal ya bayyana cewa, dan wasan gaba a kulob din Lukas Podolski zai shafe akalla mako uku yana jinya da hakan ta sa ba zai buga wasan Premier da kulob din zai yi da na Tottenham a jibi Lahadi ba.
“Ina mai bakin cikin shaida muku dan wasan gaban kulob dinmu Podolski ya samu rauni kuma zai shafe kusan mako uku yana jinya”, inji Wenger.
Sai dai labarin da ya sanyaya wa kocin Arsenal, Arsene Wenger rai shi ne na yadda daya daga cikin ’yan wasansa Jack Wilshere da shi ma ya samu rauni a lokacin wasan nashi bai yi muni kamar na Podolski ba, hasalima ana kyautata zaton zai buga wasan da kulob din zai yi da na Tottenham a jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu.
Ya zuwa yanzu, kulob din Arsenal ya farfado daga irin caccakar da ake masa na rashin tabuka abin a-zo-a-gani tun bayan da kulob din Aston billa ya doke shi a gida da ci 3-1 a wasan farko a gasar rukunin Premier da aka fara a kakar wasa ta bana.