✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Ghana Thomas Partey ya sayi wani kulob a Spain

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Spain sun  ce wan dan kwallon kasar Ghana da yake buga wa kulob din Atletico Madrid na Spain kwallo…

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Spain sun  ce wan dan kwallon kasar Ghana da yake buga wa kulob din Atletico Madrid na Spain kwallo ya sanya hannun jari tare da wadansu mutum biyu wajen mallakar kulob din Alcobendas Sport da ke wasa a rukuni na uku na ’yan dagaji a kasar.

An kafa kulob din ne a  1995 a yankin Alcobendas da ke birnin Madrid.

Thomas ya zuba hannun jari a kulob din ne tare da hadin gwiwar wadansu daga cikin masu ba shi shawara inda a yanzu ya zama wanda ya fi  yawan jari a kulob din kuma hakan ya sa ya zama shugaban kulob din.

“Na samu damar mallakar kulob din Alcobendas da ke Spain bayan na zuba jari, ina da burin daukaka martabar kulob din nan ba da dadewa ba,” inji Partey a hirar da ya yi da wata kafar watsa labarai.

Partey da takwarorinsa da suka mallaki kulob din sun fara daukar matakin farfado da martabar kulob din inda tuni suka dauki wani tsohon koci mai suna Jabi Banos aiki. Kocin ya taba horar da Partey a kulob din Atletico Madrid.

Thomas Partey ya shiga sahun ’yan kwallon Afirka  da suka mallaki kulob din kwallon kafa na kashin kansu,

Didier Drogba ne na farko bayan ya mallaki wani kulob a Amurka.

Thomas Partey mai shekara 26 yana daga cikin ’yan kwallon da ke yi wa Ghana wasa.