Da Dumi Dumi

Dan kwallon Najeriya Chukwueze ya sayi motar Naira miliyan 98

Samuel-Chukwueze

Dan kwallon Kungiyar Super Eagles ta Najeriya da yanzu yake wasa a kulob din Billareal na Spain, Samuel Chukwueze ya sayi motar da aka kiyasta kudinta a kan Naira miliyan 98.

Dan kwallon ne da kansa ya bayyana haka a shafin sadarwarsa na Instagram a karshen makon jiya jim kadan bayan kulob dinsa na Billareal ya lallasa na Leganes a gasar La-Liga ta Spain da ci 3-0.

“Na shigo gari bayan na sayi mota kirar Ferrari,” a wani sako da dan kwallon ya rubuta a shafinsa na Instagram da kuma hotonsa jingine a jikin motar.

Masana saye da sayar da manyan motoci a Intanet ne suka kiyasta kudin motar a kan Naira miliyan 98.

Samuel Chukwueze dan shekara 20 yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya da tauraruwarsu ke haskakawa.

ADVERTISEMENT

Kafin ya kama harkar kwallon kafa gadan-gadan, Chukweuze dan asalin Jihar Abiya ya yi karatu a Jami’ar Aikin Gona ta Micheal Opara da ke Umudike.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya