✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Najeriya Chukwueze ya sayi motar Naira miliyan 98

Dan kwallon Kungiyar Super Eagles ta Najeriya da yanzu yake wasa a kulob din Billareal na Spain, Samuel Chukwueze ya sayi motar da aka kiyasta…

Dan kwallon Kungiyar Super Eagles ta Najeriya da yanzu yake wasa a kulob din Billareal na Spain, Samuel Chukwueze ya sayi motar da aka kiyasta kudinta a kan Naira miliyan 98.

Dan kwallon ne da kansa ya bayyana haka a shafin sadarwarsa na Instagram a karshen makon jiya jim kadan bayan kulob dinsa na Billareal ya lallasa na Leganes a gasar La-Liga ta Spain da ci 3-0.

“Na shigo gari bayan na sayi mota kirar Ferrari,” a wani sako da dan kwallon ya rubuta a shafinsa na Instagram da kuma hotonsa jingine a jikin motar.

Masana saye da sayar da manyan motoci a Intanet ne suka kiyasta kudin motar a kan Naira miliyan 98.

Samuel Chukwueze dan shekara 20 yana daga cikin ’yan kwallon Najeriya da tauraruwarsu ke haskakawa.

Kafin ya kama harkar kwallon kafa gadan-gadan, Chukweuze dan asalin Jihar Abiya ya yi karatu a Jami’ar Aikin Gona ta Micheal Opara da ke Umudike.