✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan kwallon Najeriya ya mutu ana tsakiyar wasa

Rahoton da kafar watsa labarai da Euronews ta kalato ta nuna yadda wani dan Najeriya da ke buga kwallo a kulob din ’yan dagaji a…

Rahoton da kafar watsa labarai da Euronews ta kalato ta nuna yadda wani dan Najeriya da ke buga kwallo a kulob din ’yan dagaji a Turkiyya Ekundayo Ebenezer ya yanke jiki ya fadi ana tsakiyar wasa a ranar Lahadin da ta gabata a Turkiyya da hakan ta sa ya rasa ransa.

Rahoton ya ce a daidai minti na 35 da fara wasa ne aka ga dan kwallon ya yanke jiki ya fadi inda aka garzaya da shi asibiti, kuma a can ne Likitoci suka tabbatar da cewa ya kamu da matsalar bugun zuciya ce da hakan ya yi sanadiyyar ajalinsa.

Ekundayo Ebenezer matashi ne mai shekara 23, yana buga wa kulob din Sarayköyspor ne da ke wasa a ajin ’yan dagaji kuma ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da kulob dinsu yake karawa da na Yesilköyspor a gasar rukunin ’yan dagaji a Turkiyya kuma a daidai minti na 35 da fara wasa ne aka ga ya yanke jiki ya fadi, kuma nan da nan aka garzaya da shi asibiti, amma daga bisani rai ya yi halinsa saboda matsalar bugun zuciya.

Shugaban kulob din su Ekundayo, Feyyaz Cesen ya nuna kaduwarsa game da faruwa wannan lamari, inda ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da kuma abokan mamacin.

A wani labari makamancin wannan, kafar watsa labarai a shafin yanar gizo ta Legit.ng ta ruwaito yadda wani tsohon dan kwallon Najeriya da ke zaune a Brazil Chukwuneta Anyabolu ya rasa ransa a karshen makon jiya bayan an tsinci gawarsa a yashe ba tare da sanin dalilin rasuwarsa ba.