Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dan Majalisa ya dauki nauyin karatun dalibai 300 a Jihar Adamawa

Wani Dan Majalisar Jihar Adamawa, Alhaji  Ja’afar Magaji ya ba da gudunmawar sanya yara 300 a makarantu kyauta.

Yaran za a dauke su ne daga kananan hukumomin Mubi da Maiha, wato mazabar da dan majalisar yake wakilta.

ADVERTISEMENT

Alhaji Magaji ya bayyana cewa ya ba da gudumawar ce ganin cewa yaran yankinsa musamman wadanda rikicin Boko Haram ya shafa su samu ilimi mai inganci ta yadda za su zama yaran kwarai.

Ya kara da cewa yana son akalla mutum 100 za a dauko daga Karamar Hukumar Mubi ta Arewa, sai 100  daga Mubi ta Kudu da kuma 100 daga Maiha.

ADVERTISEMENT

Dan majalisar ya dauki alkawarin ba su isasssun tsaro daga masu garkuwa da mutane da fadan makiyaya da manoma da kuma ganin cewa ya hana shigowa da miyagun kwayoyi zuwa yankinsa.

“Zan iya iya kokarina domin ganin cewa matasa sun samu aikin yi domin zama mutanen kirki,” inji shi.

Ya yi kira ga wadanda suka amfana da tallafin su yi amfani da shi yadda ya kamata.

Dahiru Mustapha daya daga cikin wadanda suka ci moriyar tallafin,  ya ce sun yi farin samun tallafin da aka ba su, sannan ya yi kira ga sauran ’yan majalisar jihar  su yi koyi da irin wannan.

Baicin taimakon kudi da dan majalisar ya bayar, ya ba da hijabai ga matan yankinsa  da za su Hajjin bana.