✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan Majalisa ya fanso fursunoni 24 a Kaduna

Ranar Litinin dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Igabi a Majalisar Wakilai da ke Abuja, Barista Ibrahim Bello Rigachukun ya samar wa wasu firsunoni ashirin…

Ranar Litinin dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Igabi a Majalisar Wakilai da ke Abuja, Barista Ibrahim Bello Rigachukun ya samar wa wasu firsunoni ashirin da hudu (24) sa’ida yayin  da ya fanso su daga gidan yarin Kaduna.
dan majalisan ya biya musu kudaden da ake bin su ne, wanda hakan san ya aka sallame su.
Da yake jawabi ga firsunonin, Barista Bello ya ce akwai kusan fursunoni goma sha takwas da ake tuhuma da laifin kisan kai, wadanda su ma ya umurci lauyoyinsa da su taimaka wajen wakiltarsu a kotu.
Fursunonin da aka sallama ’yan gundumarsa ne da ke zama jarun. “Dukkansu matasa ne ’yan gundumata da ke tsare saboda wasu laifuffuka da suka aikata. Kuma ina ganin yawancinsu sun aikata laifuffukan ne saboda rashin aikin yi, domin kila da suna da aikin yi da ba su aikata laifuffukan ba. Wannan ya sa na ga ya dace in taimaka musu, kuma akwai wasu da ke tsare a wasu gidajen yari kamar na Zariya da sauran wurare. Na kuma umurci lauyoyina su ziyarci wuraren nan domin a tsamo su domin in taimaka wajen fito da wadanda suka aikata kananan laifuffuka domin in sama masu sana’ar yi,” inji shi.
Ya bayyana cewa yawancinsu an tsare su ne saboda sun aikata laifuffuka kamar sata ko cin amana ko fyade ko zamba cikin aminci. “Ni mutum ne da ke da son ganin mutane sun gyaru ko sun dogara da kansu. Saboda haka na ga bai kamata mu bar matasanmu a tsare a gidan yari ba, alhalin za mu iya taimaka musu da abin yi, domin su daina aikata laifuffukan da suke aikatawa,” inji shi.
Barista Bello ya tabbatar wa fursunonin da aka sallama cewa idan har suka zamanto mutanen kirki zai taimaka wajen saka su cikin Cibiyar koyar da Sana’o’i da ya kafa domin taimaka wa matasan gundumarsa.
dan Majalisar ya kuma yi kira da sauran masu hannu da shuni da kuma ’yan majalisu ’yan uwansa da su rika ziyartar gidajen yari domin su taimaka wa mutanen da suka cancanci a taimaka musu.