✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisa ya tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Katsina

Dan Majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Kankiya, Kusada da Ingawa na Jahar Katsina a Majalisar Wakilai ta Tarayya Alhaji Abubakar Yahaya Kusada, ya tallafawa al’ummomin…

Dan Majalisar mai wakiltar kananan hukumomin Kankiya, Kusada da Ingawa na Jahar Katsina a Majalisar Wakilai ta Tarayya Alhaji Abubakar Yahaya Kusada, ya tallafawa al’ummomin Kananan Hukumomin da yake wakilta wadanda matsalar ambaliyar ruwan daminar ta shafa walau ta rasa muhalli, kayan abinci, dabbobi da sauran makamantan su a kalla mutum dubu daya da dari biyar da sittin.

Da yake jawabi a wajen bayar da wannan tallafi a garin Kusada a makon da ya gabata a garin Kusada, Daraktan hukumar bayar da agajin gaggawa na kasa Mista Isiah Chonoko, bayan ya jinjinawa shi Dan Majalisar a kan irin yadda ya himmatu wajen ganin al’ummarsa da abin ya shafa sun samu wannan tallafin.

Har ila yau, Daraktan ya ce kayan tallafin da suka kawo sun hada da: Kwanon rufi bandir 1200, buhunan siminti 1,200, kusa da silin kowanne katon 120. Sai kuma buhunan shinkafa 330, wake 330, masara 330, sai buhun gishiri 80 tare da jarkokin mai 80.

Mista Isiah, ya kara da cewa, ”Samar da wadannan kaya ga jama’a kamar yadda wannan Dan majalisar ya yi ba karamin taimako ba ne.“

Dan majalisar, Honarabul Abubakar Yahaya Kusada, cewa ya yi irin wannan aikin na daya daga cikin irin aiyukansa a majalisar wakilai na ganin cewa, duk wani abin da yasan zai kawo wa mazabunsa ci gaba ya gabatar da quduri a majalisar kuma ya dage don ganin cewa, kudurinsa ya karbu kuma an aiwatar. “Ina sanar da ku cewa, ba wannan abin da ya shafi iftila’i ne kadai ke gaba na ba, kamar yadda nayi maku alkawari duk wani abin da zai kawo ci gaban mu baki daya zan yi shi. Na san ku shaidu ne ga abubuwan da suka faru a baya na batun ilmi da kiwon lafiya da sauransu. Fatan mu dai shi ne Allah Ya kiyaye abkuwar irin wannan iftila’i nan gaba.