✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya a Kudancin Kaduna

Muna amfani da wannan dama don yin kira ga jami’an tsaro da su kara tsaurara matakan tsaro a yankin.

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Jama’a da Sanga a Jihar Kaduna, Mista Nicholas N. Garba (Sarkin Noma) ya tsallake rijiya da baya daga harin ’yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne a tsakanin garin Kwoi zuwa Fadan Kagoma a Karamar Hukumar Jama’a.

An kai harin ne da misalin karfe 7:58 na dare ranar Asabar, inda aka harbi motarsa, amma babu wanda ya samu rauni.

A cikin takardar jaje da Jam’iyyar PDP ta fitar  dauke da sa hannun Sakataren Watsa Labarai na jam’iyyar a Jihar Kaduna, Abraham Aberah Catoh, bayan jajanta wa dan majalisar ta bayyana firgici kan faruwar lamarin da irinsa ne na farko a yankin.

“Muna amfani da wannan dama don yin kira ga jami’an tsaro da su kara tsaurara matakan tsaro a yankin tare da bibiyar wadanda suka shirya samamen don kamo su da hukunta su,” inji jam’iyyar

Jam’iyyar ta yi kira ga mutanen yankin su kai hankalinsu nesa tare da nisantar daukar doka a hannu, kuma ta shawarci jama’a su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da za su taimaka wajen sa ido ga duk wani motsi da ba su yarda da shi a yankin ba.