✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisa ya zama Sarkin Yakin Dan-Isan Katsina

Jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu Dan-isan Katsina Hakimin Rimaye da ke Karamar Hukumar Kankiya a Jihar Katsina Alhaji Yusuf Yakubu, zai yi nadin…

Jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu Dan-isan Katsina Hakimin Rimaye da ke Karamar Hukumar Kankiya a Jihar Katsina Alhaji Yusuf Yakubu, zai yi nadin wasu sarautu uku ciki har da Sarkin Yakinsa.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar Karamar Hukumar Kankiya Alhaji Salisu Hamza Rimaye ne za a nada a sarautar Sarkin Yakin Dan-Isan Katsina.

An haifi sabon Sarkin Yakin Dan-Isan Alhaji Salisu ne a ranar 3 ga Afrilun 1975. Ya yi firamare a Rimaye daga 1982 zuwa 1987. kuma ya yi karamar sakandare ta Je-Ka-Ka Dawo a Rimaye daga 1987 zuwa 1990.

Sai ya tafi Sakadaren Gwamnati wadda a yanzu ta koma Kwaleji a garin Funtuwa inda ya yi Babbar Sakandare daga 1990 zuwa 1993. Dan Majalisar ya zarce Kwalejin Koyon Aikin Mulki da ke Funtuwa a 1994. Kuma ya shiga Jami’ar Alkalam da ke Katsina a shekarar 2015 inda ya  yi digiri kuma har zuwa yanzu yana karatun digiri a kan sanin halayyar dan Adam.

Ta fuskar siyasa, ya shiga harkokinta tun 1998, inda ya fara da yin takarar Kansila a shekarar 2002 har zuwa 2011 amma bai ci ba.

Tsohon Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kankiya da Kusada da Ingawa Alhaji Ahmad Babba Kaita ya nada shi Mai taimaka masa na musamman. Kuma da zaben 2015 ya zo, ya sake yin takarar Dan Majalisar Jiha a karkashin tutar APC inda ya yi nasara, ya kuma sake tsayawa a bana nan ma ya yi nasara a APC.

Wata majiya ta ce kadan daga cikin dalilan da ake ganin su suka sa Dan-Isan Katsina ya ba shi sarautar Sarkin Yakin masarautarsa sun hada da cewa tunda aka zabe shi bai taba komawa wani wuri da zama ba kamar yadda wadansu ke yi. Kuma kowane lokaci a gidansa da ke Rimaye yake kwana da zarar ya taso daga aiki. Majiyar ta ce shi mutum ne mai kula da marayu da marasa karfi. Kuma shi ne dan majalisa na farko a Jihar Katsina wanda ya kafa Gidauniya mai suna “Maigemu Foundation” kuma ya dauki nauyin tafiyar da ayyukanta. Wasu daga cikin ayyukan gidauniyar akwai, tallafa wa mutanen yankinsa kan abin da ya shafi karatu da sauransu. Kuma duk lokacin bikin Sallah yakan dinka wa marayu da marasa karfi da suka fito daga karamar hukumar kayan Sallah, bayan kayan azumi da sauransu. An shaide shi da jajircewa kan duk wani abin da ya san na ci gaba ne ga al’ummarsa.

Sabon Sarkin Yakin Dan-Isan Katsinan, shi ne Mataimakin Mai Tsawatarwa a Majalisar Dokokin Jihar Katsina.

A cewar wata majiya ta kusa da fadar Dan-Isan Katsina sarautar Sarkin Yaki ana ba da ita ce ga gwarzo, jarumi, mai juriya a fagen daga a masarautun gargajiya a lokacin da ake yake-yake. Kuma Sarkin Yaki mutum ne da yake daya daga cikin amintattun sarki kuma mai kare masarauta daga abokan gaba. Kazalika sarauta ce wadda mafi yawan lokuta akan yi gadonta sai fa inda babu ita a baya,to ana bayar da ita ga wanda ya dace.

Majiyar ta ce, amma yanzu da babu yaki masarautu na bayar da ita ce ga mutumin da suka lura da ya yi ko yana aiwatar da irin wancan aiki na baya ko makamancinsa. Kuma sarauta ce wadda aka fi samunta a karkashin sarki kawai. “Juyin zamani ya kawo hakimai ke yin nada irin wannan sarauta bayan sun samo izini daga Sarki,” inji majiyar.