✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan majalisar Bauchi ya kamu da Coronavirus

Dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Toro da Jama’are a Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Tukur Ibrahim ya kamu da cutar coronavirus. Kakakin Majalisar Abubakar…

Dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Toro da Jama’are a Majalisar Dokoki ta Jihar Bauchi, Tukur Ibrahim ya kamu da cutar coronavirus.

Kakakin Majalisar Abubakar Sulaiman ya bayyana hakan yayin zamansu na musamman a ranar Litinin bayan dawowarsu daga hutu.

A cewarsa, yanzu haka Tukur Ibrahim na a daya daga cikin cibiyoyin killace masu cutar a jihar inda yake samun kulawa.

Kakakin majalisar ya ce tuni aka dauki jinin wasu daga cikin ‘yan majalisar domin su ma a yi musu gwajin, yana mai shawartar ragowar da su ma su bi sahu.

Daga bisani Abubakar Sulaiman ya jagoranci addu’a ta musamman domin neman sauki ga Tukur Ibrahim.

Idan za a iya tunawa, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed da mataimakinsa Sanata Baba Tela sun taba kamuwa da cutar kafin daga bisani gwamnan ya warke.