Da Dumi Dumi

Dan Majalisar Dattawa a Amurka ya kamu da COVID-19

Sanata Rand Paul
Sanata Rand Paul ya ce bai san ya yi mu'amala da wani mai dauke da cutar ba

A karo na farko an samu wani dan Majalisar Dattawan Amurka da ya kamu da cutar COVID-19 wadda Coronavirus ke haddasawa.

Wani sako da aka wallafa a shafin Twitter na Sanata Rand Paul mai wakiltar jihar Kentucky a majalisar ya ce tuni dan majalisar ya killace kansa.

Sakon ya kuma ce Mista Paul, wanda likita ne, bai “nuna wasu alamun kamuwa ba, amma saboda yawan taka-tsantsan ya yi gwaji bisa la’akari da yawan tafiye-tafiyen da yake yi da kuma yawan tarurrukan da yake halarta”.

Dan majalisar ya kuma ce yana fatan komawa bakin aiki da zarar wa’adin killace kan da ya yi ya cika.

Da ma dai an samu wasu ’yan Majalisar Wakilai biyu, Mario Diaz Balart da Ben McAdams, sun kamu da cutar, kamar yadda kafofin yada labarai na Kasara suka ruwaito.

ADVERTISEMENT

Majalisar Dattawan ta Amurka dai ta yi wani zama ranar Lahadi da nufin zakulo hanyar tunkarar kalubalen da Coronavirus ta zo da shi.

Sai dai kuma Sanata Rand Paul ya ce kwana 10 da suka wuce daga gida ma’aikatan ofishinsa na Washington DC ke aiki, don haka babu yiwuwar wani ya dauki kwayar cutar daga gare shi.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya