✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Majalisar Mazabar Lame ya dauki nauyin duba masu ciwon hakori 377

Likitoci da jami’an da kiwon lafiyar hakora da sauran cututtukan baki, sun duba masu fama da ciwon hakori da sauran cututtukan baki su 377, a…

Likitoci da jami’an da kiwon lafiyar hakora da sauran cututtukan baki, sun duba masu fama da ciwon hakori da sauran cututtukan baki su 377, a yankin Lame da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi a karshen makon nan.

Wannan aiki da a ka gudanar a asibitin garin Rishi, an gudanar da shi ne a karkashin shirin wayar da kan jama’ar yankin, kan muhimmancin kula da lafiyar baki da dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, mai wakiltar yankin Alhaji Bala Abdu Rishi ya dauki nauyin gudanarwa.

Da yake zantawa da wakilinmu babban likitan da ya jagoranci likitocin da suka gudanar da aikin, Dokta Abdullahi Sa’idu  da ke Sashin Kula da Lafiyar Hakora na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, ya ce  aiki da suka gudanar, wata  dama ce da dan majalisar yankin ya ba su, domin su zo su yi wa  al’ummarsa aiki, lura cewa akwai  illoli da suke shafar hakori da baki a  yankin.

Ya ce babu shakka fannin jinyar hakori yana daya daga cikin abubuwan da mutane suke watsi da shi.

Ya ce yana da kyau a rika ilimantar da jama’a kan kula da cututtukan baki. Domin kashi 60 zuwa 70 cikin 100  na cututtukan,  mutum zai iya kare su,  ta hanyar wanke baki da magogi ko da asuwaki.

Likitan ya ce a wannan aiki da suka gudanar sun wayar da kan jama’a kan cututtukan baki da  ayyukan  duba baki da hakora.

A zantawarsa da wakilinmu dan majalisar, Alhaji Bala Abdu Rishi ya ce abin da ya sa ya dauki nauyin gudanar da wannan shiri, na duba masu fama da matsalar cututtukan baki musamman  ciwon hakori shi ne ganin yadda ake fama da wadannan matsaloli a  yankin.

“Wadannan matsaloli suna faruwa ne, saboda rashin ilimantarwa. Don haka muka yi magana da likitocin hakora na roki su, zo su ba da gudunmawarsu, ta hanyar bayar da magani da ilimantar da jama’a kan kula da baki baki daya,’’ inji shi

Alhaji  Bala Abdu Rishi ya yi bayanin cewa ba ya ga wannan aiki, akwai ayyuka da dama da ya  gudanar a mazabar da suka hada da gina masallatai da gadoji da  bude  makarantun firamare a kauyukan Unguwar Sule da Yayaka da jan wutar lantaki a wasu kauyuka da daukar nauyin biyan kudaden yi wa yaran yankin  sama da 70 rajista a manyan makarantun da ke  Misau da Azare da ATAP da Kangere da ke Jihar Bauchi.

A zantawarsa da wakilinmu Sardaunan Rishi Alhaji Sabo Yusuf  ya yaba wa dan majalisar kan wannan kokari da ya yi. Ya yi  kira ga sauran wakilai da suke kan kujera su rika yin koyi da irin wannan al’amari na taimaka wa al’umma.