Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Dan majalisar PDP ya sha alwashin yin kyakkyawan wakilci

PDP-logo

Zababben dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Karamar Hukumar Jama’a, Mista Ali Kalat ya sha alwashin gudanar da kyakkyawan wakilci tare da tafiya da kowa ba tare da nuna wariyar jam’iyya ba.

Dan majalisar na Jam’iyyar PDP ya ce bisa ga irin kyakkyawan kaunar da jama’ar karamar hukumar suka nuna masa, zai tsaya bisa ga alkawurran da ya yi wa al’ummar mazabarsa.

ADVERTISEMENT

“Ina so in tabbatar muku cewa zan gudanar da wakilcina ta hanyar tuntubar kowace gunduma cikin jama’ar da nake wakilta tare da aiwatar da abin da ya dace da kowace gunduma da mazaba da ke karkashina don samar musu da abubuwan ci gaba. Wannan, baya ga ainihin aikin da aka san dan majalisa da shi ne na yin dokoki,” inji shi

Dan majalisar ya yi kira ga jama’ar mazabarsa su guji suka mara amfani ga shugabanninsu maimakon haka su ba shi hadin kai. Sannan ya bukaci malaman addini da sarakunan gargajiya da sauran kungiyoyi da jami’an tsaro su ba shi cikakken goyon baya a wakilcin da zai gudanar karo na farko.

ADVERTISEMENT