✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

dan Majalisar Wakilai na Chanchaga ya bayar da gudunmawar tiransifoma 13

dan Majalisar Wakilai na mazabar Chanchaga, Malam Muhammad Umar Bago ya bayar da gudunmuwar na’urorin rarraba wuta [tiransifoma] guda 13 masu darfin 500KbA ga unguwannin…

dan Majalisar Wakilai na mazabar Chanchaga, Malam Muhammad Umar Bago ya bayar da gudunmuwar na’urorin rarraba wuta [tiransifoma] guda 13 masu darfin 500KbA ga unguwannin da ke fama da matsalar darancin wutar lantarki.
dan Majalisar, wanda babban hadiminsa, Malam Adamu Aliyu Muhammad ya wakilta, ya tabbatar da dasa guda 4 a unguwannin Nasarawa A da Tayi da Fadikpe kuma ya bayar da tabbacin za a dasa sauran guda 9 din a yankunan da suka fi budata.
Malam Adamu Aliyu ya jaddada cewar dan Majalisar yana ayyukan da ya ayyana gudanarwa a lokacin yadin neman zabe don cika aldawari, musamman ma muhimman fannonin da suka shafi ilimi da kiwon lafiya da shirin tallafa wa mata da matasa da kuma ruwan sha.  
Daga cikin ayyukan da ya gudanar, dan Majalisar ya samar da rijiyoyin tuda-tuda da masu amfani da hasken rana kusan guda 100,wadanda akasarinsu suna aiki, kuma za a gyara wadanda suka tsaya.  Sannan a bana an yi tanadin samar da guda 50 kafin darshen shekara.
A fannin ilimi kuwa, dan Majalisar ya gina azuzuwa a wasu makarantun firamare kuma ya ba da aikin gyara wasu. Sannan ya yi nufin gudanar da wadansu ayyuka daban-daban a wadansu makarantun, duk don a samar da kyakkyawan yanayin koyo da koyar da dalibai.
Wakilin dan Majalisar ya bayar da tabbacin za a horar da mata da matasa sana’o’in da suke sha’awa wadanda za su taimaka musu dogaro da kai domin za a samar musu jarin da za su gudanar da su.
Ya shawarci jama’ar da suka samu damar cin moriyar muhimman ababen da aka samar musu na rayuwa, su sa ido wajen kula da su don amfanin kansu na tsawon lokaci.
Ya budaci wadanda ba su samu ba su dara haduri don ana bin abin ne a hankali, bisa tsari ta yadda jama’a da dama za su amfana.
A darshe ya nemi a ci gaba da ba shi shawarwarin da suka dace don ciyar da yankin gaba, wanda shi ne babban dalilin da yake wakiltarsu a majalisa.