Da Dumi Dumi

Dan Najeriya da ke kwallon Kwando a Amurka ya nutse a ruwa

Wani dan Najeriya Calistus Anyichi da ke karatu kuma yake buga Kwallon Kwando a Amurka ya rasu a cikin wani kogi bayan ya nutse.

Al’amarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta wuce kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Calistus, ya je wurin shakatawa na Buttermilk Falls State Park ne da ke birnin New York na Amurka inda ya fada wani kogi don yin wanka, kuma tunda ya nutse a ruwan ba a sake jin duriyarsa ba sai gawarsa aka tsinto a can wani wuri.

Anyichi dai dalibi ne a Jami’ar Binghanton da ke Amurka kuma yana daga cikin ’yan kwallon kwando a jami’ar inda hakan ya sa ya yi suna.

Rahotanni daga jami’ar sun ce an tsinci gawar marigayin ne da misalin karfe biyar na yamma a ranar Lahadin bayan ruwa ya ja gawarsa zuwa wani waje mai tazara daga wajen shakatawar.

ADVERTISEMENT

Tommy Dempsey, kocin kulob din Kwallon Kwando na Jami’ar Binghanton a bangaren maza ya tabbatar da rasuwar Anyichi.

“Mun yi bakin cikin rashin Anyici domin matashi ne mai hazaka da za mu dade ba mu maye gurbinsa ba. Ya koma ga Allah kuma babu yadda za mu yi sai dai mu yi masa addu’a,” inji wata sanarwa da kocin ya sanya wa hannu kuma aka raba wa manema labarai.

Calistus Anyiechi dan asalin Najeriya ne da iyayensa suka haifa a Najeriya amma suka koma Amurka.

Share