✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Najeriya ne ya kirkiro rigakafin COVID-19 a Amurka

Likitan dan Najeriyan shi ne mutum na farko da ya samar da rigafin Covid-19 mafi inganci

Wani likita dan Najeriya Dokta Onyema Ogbagu ne ya kirkiro rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer na kasar Amurka ya samar.

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya sanar da haka, tare da cewa rigakafin shi ne mafi inganci kuma na farko da aka samar a Amurka domin cutar COVID-19.

“‘Yan Najeriya sun ba wa duniya gudunmuwa ta fuskoki da dama. Muna matukar jinjina ga Dokta Onyema Ogbuagu da ya taimaka aka samar da rigakafin COVID-19”, inji Ofishin.

Ofishin jakandancin ya sanar da haka ne ta shafinsa na Twitter ranar Litinin.

Dokta Onyema ya yi digirinsa na farko ne a Jami’ar Kalabar a shekarar 2003, kuma Farfesa ne a fannin da ya shafi magani da cuttuka masu yaduwa a Jami’ar Yale da ke Amurka.