Wani matashin dan kwallo dan asalin Najeriya mai suna Semi Ajayi, ya sanya wa kulob din Arsenal da ke Ingila hannu.
Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa da kulob din ya fitar a kafar sadarwarsa a karshen makon jiya.
Bayanin ya ce kulob din ya sayi dan kwallon ne bayan ya haskaka a wasanni biyu a matsayin gwaji da kulob din ya yi masa a kwanakin baya.
Shi dai Ajayi ya taba bugawa kulob din Charlton Athletic kafin kulob din ya raba gari da shi a karshen kakar wasan da ta wuce.
Daga nan ya canza sheka zuwa kulob din Norwich gab da za a fara kakar wasa ta bana daga bisani ya ziyarci kulob din Arsenal a matsayin gwaji. Wasanni biyu da ya buga a matakin yara a kulob din Arsenal ta sa kulob din ya gamsu da kwazonsa inda ya yanke shawarar dauke shi.
A halin da ake ciki Semi Ajayi, ya sanya hannu a kwantaragin shekara biyu a kulob din na Arsenal sai dai kulob din bai bayyana albashin da dan kwallon zai rika karba ba.
Ajayi ya taba bugawa Najeriya kwallo a matakin yara, don haka zai iya bugawa Ingila kwallo tun da an haife shi ne a garin Crayford na Ingila.
Ajayi, yana wasa ne a bangaren baya (defender).
Dan Najeriya ya sanya hannu a kulob din Arsenal
Wani matashin dan kwallo dan asalin Najeriya mai suna Semi Ajayi, ya sanya wa kulob din Arsenal da ke Ingila hannu.Bayanin haka na kunshe ne…