Da Dumi Dumi

‘Dan Sarki da ’yan mata hudu’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe  da fatar ana cikin koshin lafiya. Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin ‘Dan Sarki da ’yan mata hudu.’ Labarin ya kunshi yadda saukin kai ke janyo nasara. A sha karatu lafiya.

Taku; Amina Abdullahi

Akwai wani dan Sarki da ya dawo daga kasar waje bayan ya kammala karatu.  Mahaifinsa yana son ya je gidan Malam Bala mijin Hajiya Delu don ya auri daya daga cikin ’ya’yansu saboda ya yaba irin tarbiyyarsu. Da farko dan Sarkin bai so haka ba amma ganin mahaifinsa na kula da shi yadda ya kamata ya yanke shawarar zuwa ganin wadancan ’yan mata da ake magana a kansu.

Dan Sarki ya hada baki da kanwarsa cewa zai je gidan su Hajiya Delu amma a matsayin mai aikin gida don ta wannan hanyar ce kawai zai iya gane irin tarbiyyar ’yan matan da  hankalinsu.

Da ya isa gidan ya roki su Hajiya Delu a taimaka masa ya zama mai aikin gida, ta hanyar yin wanke-wanke da shara da sauran aikace-aikacen gida.  Nan take Hajiya Delu ta amince ba tare da sanin ita da ’ya’yansu mata cewa dan Sarki ne ba. Mu kwana nan

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya