✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan Sarkin Hausawan Kwatano ya rasu

Dan Sarkin Hausawan Kwatano  da ke Jamhuriyyar Benin Muhammadu Mouniru Khalifa ya rasu. Marigayi Khalifa mai shekara 15 ya rasu ne a wani asibiti a…

Dan Sarkin Hausawan Kwatano  da ke Jamhuriyyar Benin Muhammadu Mouniru Khalifa ya rasu. Marigayi Khalifa mai shekara 15 ya rasu ne a wani asibiti a garin Kwatano bayan ya yi rashin lafiya. Kuma an yi masa jana’izar ce a harabar Babban Masallacin Juma’a na Unguwar Zango a garin Kwatano.

Da yake bayani kan wannan rashi, Sarkin Hausawan Kwatano, Alhaji Muhammadu Mouniru Garba Nakura ya mika godiya ga daruruwan jama’a Musulmi da Kirista da suka yi tattaki daga kasashe masu makwabta da Benin zuwa birnin Kwatano domin halartar jana’izar dansa Muhammadu Mouniru Khalifa da aka yi a ranar Talata da ta gabata.

Sarkin Hausawan Kwatanon ya ce, “A yayin da nake cikin bakin cikin wannan rashi na dana Muhammadu Mouniru Khalifa da Allah Ya karbi ransa a ranar Talata da safe, a daidai wannan lokaci ina godiya ga Allah tare da mika godiya ga dimbin al’ummar Najeriya Musulmi da Kirista da suka fito daga kabilu daban-daban kuma suke zaune a wasu kasashen Afirka makwabtanmu da suka zo nan Kwatano domin halartar jana’izar wannan yaro tare da yi mana ta’aziyya.”

Jama’a sun rika tururuwa zuwa Fadar Sarkin Hausawan Kwatano don yi masa ta’aziyya, lamarin da ya kawo tsayuwar al’amura a Unguwar Zango da ke birnin.