Da Dumi Dumi

Dan shekara 12 ya fara karatun jami’a a Ghana

Viemans Bamfo, mai shekara 12 da ya shiga jami’a a Ghana
Viemans Bamfo, mai shekara 12 da ya shiga jami’a a Ghana

Biemans Bamfo mai shekara 12 dan kasar Ghana ya janyo ka-ce-na-ce a shafukan sada zumunta bayan da ya bayyana cewa ya samu gurbin shiga jami’a.

Yanzu haka dai Bamfo ne mafi karancin shekaru a cikin dalibai 2900 da suka samu gurbin shiga jami’a a kasar a bana.

Biemens Bamfo dai bai ci gaba da sakandare ba bayan kare firamare, inda mahaifansa ke koya masa karatu a gida. Daga nan ne kuma ya rubuta jarrabawar kammala karatun sakandare, inda ya samu kyakkyawan sakamakon WASSCE.

Tuni ya fara karatu a sashen Harkokin Mulki (Public Administration) a Jami’ar Ghana.

Hakan ne ya sa masu amfani da kafafen sada zumunta suka yi ta sukar al’amarin, inda suke bayyana mamakinsu kan yadda yaron da bai yi sakandare ba zai lashe jarrabawar sakandare kuma har ya shiga jami’a.

ADVERTISEMENT

BBC ya ruwaito.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya