✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan takarar ya nemi kotu ta kwato masa kudinsa a wurin wakilan jam’iyya

A farkon wannan mako ne wani da ya nemi tsayawa takarar  Majalisar Tarayya a Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa, Barista Iliya Aliyu ya yi karar…

A farkon wannan mako ne wani da ya nemi tsayawa takarar  Majalisar Tarayya a Jam’iyyar APC a Jihar Nasarawa, Barista Iliya Aliyu ya yi karar wadansu kansiloli 7 a kotu, inda ya bukaci kotun ta karba masa kimanin Naira miliyan 7 da ya raba wa wakilan jam’iyya (daliget) don su zabe shi a  zaben fid-da-gwani na jam’iyyar da aka yi.

Dan takarar wanda ya so wakiltar mazabar Akwanga da Wamba da Nasarawa-Eggon a Majalisar Tarayyar ya gabatar da karar ce a Kotun Majistare da ke Akwanga. Takardar karar da aka karanta a kotun ta ce kansilolin sun ziyarce shi ne a gidansa suka bukace ya ba su Naira miliyan 8 don su raba wa wakilan jam’iyya a mazabar don su kada masa kuri’a.

Ya ce nan take ya ba su kudin, amma maimakon su zabe shi sai suka zabi abokin karawarsa, inda a karshe ya gano ba su kada masa kuri’a ba. A cewarsa bayan ya tuntubi wadansu daga cikin wakilan jam’iyyar sun amince ba su kada masa kuri’a ba, suka mayar masa da kudinsa da ya kai Naira miliyan daya, yayin da wadansu kuma suka ki mayar masa da kudin nasa.

Shi ya sa a cewarsa yake so kotu ta karbo masa ragowar kudinsa Naira miliyan 7 daga wurin kansilolin don su suka bai wa wakilan. Bayan an karanta wa wadanda ake zargin takardar karar sun musanta zargin, inda suka ce ba su suka bukaci dan takarar ya ba su kudin don su raba wa wakilan  ba kamar yadda ya bayyana.

A cewarsu shi ya gayyace su zuwa gidansa inda bayan ya nemi goyon bayansu daga bisani da za su tafi sai ya ba su kudin ya ce su raba wa wakilan don su zabe shi. Kuma sun cika masa alkawari don sun raba wa da wakilan jam’iyyar kudin. Sai dai a cewarsu ba su san ko sun kada masa kuri’a ko ba su yi ba, domin yadda aka tsara zabubbukan babu wanda zai iya gano hakan a cewarsu.

Bayan alkalin kotun Mai Shari’a Abdul Alhassan ya saurari bangarorin biyu, ya daga zaman shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Nuwamban da ke tafe.

A zantawarsa da wakilinmu, daya daga cikin kansilolin da aka kai kararsu kotun, wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce “Ba shakka ina cikin wadanda aka kai kararsu kotun, amma a gaskiya ba na cikin wadanda suka karbi kudi daga wajen dan takarar. Idan kuma yana da shaidar da zai tabbatar na karbi kudinsa sai ya gabatar da a gaban kotu.”

Haka wakilinmu ya gano cewa wadansu wakilai da magoya bayan wani da ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar APC (an sakaye sunansa) suna bin wadansu wakilan jam’iyya har gidajensu don su mayar da kudin da suka karba wajen ubangidansu tunda ba su zabe shi ba.

Wata majiya ta bayyana wa wakilinmu cewa kodayake babu  tabbacin ko dan takarar ne ya turo su karbi kudin, amma a cewar majiyar abin da ke faruwa ke nan a yanzu. Wakilinmu ya kuma gano wadansu magoya bayan Mista Thomas Ogilla wanda ya sha kaye a zaben fid-da-gwani na APC da zai wakilci mazabar Akwanga ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar sun tuntubi wasu daliget don su mayar musu da kudin da suka karba, har ma wadansu daga cikinsu sun mayar da kudin bayan magoya bayan dan takarar sun yi musu barazanar turo musu ’yan bangar siyasa  suyi musu wulakanci.

Haka kuma wakilinmu ya gano cewa wani tsohon shugaban riko na Karamar Hukumar Akwanga, wanda ya nemi takarar  dan Majalisar Dokokin Jihar a mazabar Akwanga ta Tsakiya a APC kuma ya fadi a zaben fid-da-gwanin, ya umarci magoya bayansu su bi wadansu wakilan jam’iyya su karbo masa kudinsa tunda sun ki zabarsa.

Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa dan takarar ya turo wadansu wakilansa ne su sa ido a kan yadda zaben ke gudana, inda daga baya suke bin wadanda suka gano ba su kada masa kuri’a ba su mayar masa da kudinsa.

A Nasarawa-Eggon ta Yamma wani da  ya nemi tsayawa takarar Majalisar Dokokin Jihar a APC ya bukaci wadansu na kusa da shi su karbo masa kudinsa daga wakilan jam’iyya na mazabarsa bayan sun ki su zabe shi. Tun  farko dan takarar ya ki amincewa da sakamakon zaben, inda ya zargi babban jami’in zabe na APC da kin bai wa ’yan takarar sunayen wakilai su gani.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan wakilan jam’iyyar sun karbi kudaden ne daga ’yan takarar amma kuma a ranar zaben sai suka zabi wadanda suke so.