Search
Subscribe
Dan takarar ’yan Hamayya a Nijar ya bayyana shakku kan tsarin zabe

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Dan takarar ’yan Hamayya a Nijar ya bayyana shakku kan tsarin zabe

Tsohon Shugaban Nijar, kuma dan takarar gamayyar jam’iyyun adawa na ADR a zaben Shugaban Kasa na 2021 Alhaji Mahaman Usman ya nuna fargaba dangane da tsare-tsaren zabubbukan da ke tafe, inda ya bukaci ’yan kasar su tashi tsaye don murkushe duk wani magudin zabe.

Tsohon Shugaban Kasar wanda ya jagoranci wani gangamin magoya bayan gamayyar jam’iyyun adawa ya nuna shakku game da tsare-tsaren zaben 2020 da 2021 bisa la’akari da yadda dan takarar Jam’iyyar PNDS TARAYYA mai mulki Bazoum Mohammed ke ci gaba da rike mukaminsa na Minstan Cikin Gida, bayan batun kwangilar hada kundin rajista da aka bai wa wani kamfani cikin yanayi mai cike da rudu.

Alhaji Mahaman Usman ya gargadi magoya bayansa da  daukacin ’yan Nijar su tashi tsaye don taka wa masu mulki birki a yunkurinsu na maimaita abin da ya kira magudin da ya dabaibaye zaben 2016.

Shugaban kawancen jam’iyyun FPR, Ibrahim Yakuba da ke cikin ’yan siyasar da suka halarci gangamin na gamayyar ADR ya yi na’am da kiran na takwaransa.

Da yake mai da martani a kan zarge-zargen ’yan adawar, Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar PNDS mai mulki Asumana Mahamadu ya yi watsi da zarge-zargen da cewa soki-burutsu ne kawai.

Wannan dambarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage wata 10 kafin zaben kananan hukumomi, kuma zagayen farko na zaben Shugaban Kasa da na Majalisar Dokokin zai gudana nan da wata 22 masu zuwa kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin