✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan wasan Arsenal Mkhitaryan ya samu karaya

A ranar Litinin da ta gabata ce kulob din Arsenal da ke Ingila ya bayar da sanarwar  cewa dan wasansa Henrikh Mkhitaryan zai kwashe kimanin mako…

A ranar Litinin da ta gabata ce kulob din Arsenal da ke Ingila ya bayar da sanarwar  cewa dan wasansa Henrikh Mkhitaryan zai kwashe kimanin mako 6 yana jinya saboda karayar da ya samu a kafarsa ta dama.

Dan shekara 29, Mkhitaryan yana daga cikin ’yan wasan da ke buga wa Arsenal kwallo kusa koyaushe a karkashin sabon koci Unai Emery.

Ya samu karayar ce a wasan da kulob din Tottenham ya lallasa na Arsenal da ci 2-0 a gasar Firimiya a ranar Asabar da ta wuce.

An canja dan kwallon ana gab da tafiya hutun rabin lokaci a yayin wasan, saboda raunin da ya samu.  Bayan likitoci sun duba shi ne aka tabbatar ya samu karaya a kafarsa ta dama inda hakan zai sa ya shafe akalla mako 6 yana jinya.

Ana sa ran a watan Fabrairun 2019 ne dan wasan zai koma fagen wasa.