✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dan wasan barkwanci ya zama Shugaban Kasa

Dan wasan barkwanci a talabijin mai suna Bolodymyr Zelensky ne ya lashe zaben Shugaban Kasa zagaye na biyu a kasar Ukraine. Zelensky, ya samu sama…

Dan wasan barkwanci a talabijin mai suna Bolodymyr Zelensky ne ya lashe zaben Shugaban Kasa zagaye na biyu a kasar Ukraine.

Zelensky, ya samu sama da kashi 70 cikin 100 na kuri’ar da aka kada  inda ya doke Shugaban Kasa mai ci Petro Poroshenko.

Tuni dai Poroshenko ya karbi shan kaye, amma ya ce ba zai hakura da siyasa ba.

A jawabinsa na farko, Zelensky ya ce yana son ya kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da ’yan aware a Gabashin Ukraine. Ya ce zai ci gaba tatattauna yarjejeniyar Minsk, zuwa bin matakan da suka shafi tabbatar da tsagaita wutar.

Wakilin BBC a Kieb ya ce sabon Shugaban zai fuskanci kalubale kan yadda zai nuna wa ’yan kasar da duniya baki daya cewa ya san me yake yi.

Mista Zelensky wanda sabo ne a siyasa, an fi saninsa da wasan ban dariya a talabijin, inda ya yanzu ya zama Shugaban Kasa.