✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangantakar kasa da dan Adam a rayuwa

Assalamu alaikum ya ma’abuta wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Kamar yadda muka gani a sama, yau dai za mu yi nazari ne game da dangantakar…

Assalamu alaikum ya ma’abuta wannan fili na Sinadarin Rayuwa. Kamar yadda muka gani a sama, yau dai za mu yi nazari ne game da dangantakar da ke tsakanin dan Adam da kuma kasa, sannan mu duba tasirin ita kanta kasar da kuma yadda ta shafi al’amuranmu da kuma rayuwarmu gaba daya.

Tun farko dai kamar yadda muka gani ko muka karanta daga littattafai saukakku, asalin mutum dan Adam daga kasa ne. Idan za mu kara nazari, sai mu ce shi dai kakanmu, Adamu (AS), an halicce shi ne daga tabo, watau kasa ke nan, wanda daga gare shi ne kuma aka halitta masa abokiyar zamansa, watau Hauwa’u ke nan.

Bayan sun sauko bisa doron kasa, sai komai nasu ya kaasance daga kasa. Ruwan da suka sha, daga kasa ne domin kuwa masana kimiyya sun samu tabbacin cewa ruwan da ake yi na sama ma, daga kasa yake tashi bisa hukuncin Allah, sannan a sauko da shi a matsayin ruwan sama. Baya ga ruwa, tsirrai, wadanda su ne ke kasancewa abincin dan Adam, daga kasa suke. Dabbobin da ke samar da nama da sauran sinadaran da ke taimaka wa dan Adam, su ma daga kasa suke. Gidan da dan Adam ke kwanciya a ciki daga kasa yake.

Abin hawa da kan taimaki dan Adam yin zirga-zirga daga wannan wuri zuwa wancan wuri, watau kamar keke, babur, mota, jirgin kasa, jirgin ruwa, jirgin sama da duk sauran karafa da dan Adam ke amfani da su wajen tasarrufin al’amuransa na duniya, duk daga kasa suke. Duk wani nau’in abinci, wanda ya hada da shi kansa abincin, kamar man gyada, manja, gishiri, kanwa, kuka, tumatiri, barkono, albasa da sauransu, duk daga kasa suke.

Ba wannan ba ma, hatta suturar da mutane ke sanyawa domin kwalliya da kuma kare tsiraici, duk daga kasa suke, watau daga auduga da sauran sinadarai. Don haka, bari mu yi ta babban mahaukaci, duk wani abu da muke gani a doron kasa, to babu shakka mafarinsa da samuwarsa daga kasar ya fito. Don haka, dan Adam da dukkan abin da ya mallaka a duniyar nan kasa ne kuma ya zuwa kasar ne makomarsa.

Babu makankara ga wannan batu na sama, cewa komai kasa ne a duniyar nan, kuma karshensa kasa. Mutum, wanda shi ne mafificin halitta a duniyar nan, da kasa aka halitta shi, kuma karshensa kasa zai koma, idan ya mutu ke nan. Abincin da mutum ke ci a cikinsa, daga kasa ya fito, kuma idan ya kasayar da shi, kasa yake komawa, sannan ya zama taki ya sake rikida zuwa abinci. karafan da ake sarrafawa su zama na’urori daban-daban da ababen hawa iri daban-daban, asalinsu daga kasa suke, kuma daga karshe rubewa za su yi su koma kasa. Ruwan da mutum ya sha ko ya yi amfani da shi ta kowace hanya, daga kasa yake, kuma daga karshe, a kasar zai koma.

Idan mun fahimta da wannan tariya da nazari, sai kuma mu zo mu duba darussan da bayanin nan ke nuna mana. Babban abin da ya kamata mu fahimta shi ne, mu gane cewa ashe da duniyar nan, da mu kanmu ’yan Adam, da duk abin da ke cikinta kasa ne, kuma daga karshe kasar za mu koma. Idan haka ne, me ya kamata mu yi? Kamata ya yi mu natsu, mu bi rayuwar nan a sannu, ba tare da mun wahalar da junanmu da kawunanmu zuwa wani abu marar amfani ba.

Mu gane cewa, ruhin da ke jikinmu, shi kadai ne mai amfani, shi kadai ne ba kasa ba. Shi kuma ruhi ko rai, babu ruwansa da abinci ko abin sha. Idan ka kasance mai hadamar tara dukiya, kana tara dinbin kasa ne, domin daga kasa take kuma can za ta koma. Idan ka zama mai cutar dan uwanka da ha’intarsa a rayuwa, ka yi ha’incin nan ne ga kasa, kuma abin da ka ha’intar nan kasa zai kasance. Sai dai a yayin da ka yi wannan, ke nan ka saka ruhinka cikin fitina, domin daka karshe ruhin naka ne zai cutu, kamar yadda ka cutar da ruhin gangar jikin wani ko wata.

Babbar fa’idar da muke so a fahimta daga wannan maudu’i shi ne, mu yi karatun natsuwa daga al’amuran rayuwa, mu sanya fahimta daga abubuwan da ke wahalar da mu, al’amuran da ke sanya mu cikin fitina da rashin kwanciyar hankali. Me ke nan? Amsar dai ita ce kasa. Don haka kada mu biye wa kasa har ta halakar mana da ruhi, ta hana mu sukuni da jin dadin kwanciya a gidan duniya da kuma gidan gobe. A duk lokacin da mutum ya shiga rashin jin dadi, ba gangar jiki ce ke wahala ba, ruhi ne ke wahala, domin kuwa da makomar gangar jiki da makomar kudi ko wata dukiya ko wata kadara, duk daya ne. Alhali makomar ruhi daban take, kasancewar ita dukiya da gangar jikin dan Adam, duk kasa za su koma, alhali ruhin dan Adam, shi zai daukaka ne zuwa inda Allah Ya kadarta masa, domin shi ba kasa ba ne.

Da fatan mun fahimci karatun da ke cikin wannan maudu’i, nake cewa mu huta lafiya, sai kuma mako mai zuwa, idan Allah Ya kai mu.