✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangantakar Nahawu da Ka’idojin Rubutu (1):

Nazari kan bambancin ma’ana a tsakanin kalmomin: ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa   A wannan mako Aminiya ta kawo muku wata makala ce kan…

Nazari kan bambancin ma’ana a tsakanin kalmomin: ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa

 

A wannan mako Aminiya ta kawo muku wata makala ce kan dangantaka da ke tsakanin Nahawu da ka’idojin rubutu, wanda nazari ne kan bambancin ma’ana a tsakanin kalmomin ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa. Malam  Aminu M.B. Umar, ya rubuta makalar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na duniya da Jami’ar Jihar Kaduna ta shirya, ranar 14 zuwa 17 ga Nuwamban bana:

 

Ma’anar Nahawu

Nahawu, a kowane harshe, ana nufin yadda tsarin wannan harshe yake, tun daga yadda kalmominsa suke da yadda suke haduwa da juna bisa tsari don su samar da ingantattun jumloli masu ma’ana, daidai da yadda masu wannan harshe ke sarrafa shi a cikin harkokinsa na yau da kullum (Bello, A. 2014).

Shi ko Nahawun Hausa, a fahimtar Bello, A. (2014) na nufin yadda kalmomin Hausa ke bayyana cikin wani tsari don bayar da ingantattun jumloli, wadanda Bahaushe zai karba kai-tsaye ba tare da wata ja-in-ja ba.

Sani (1999) ya bayyana Nahawu a matsayin fannin ilimi na kimiyyar harshe wanda ya danganci ginin jumla. Jumla kuwa, magana ce cikakkiya mai ma’ana, wadda aka gina bisa wasu k’aidojin harshen na musamman. Kalmomi su ne tubalan gina jumla.

Shi ko Muhammad(2009), cewa ya yi‚ Nahawu shi ne dokokin tafiyarwa ko sarrafa harshe a ka’idance.

Daga wadannan bayanai da muka samu daga masana, za mu iya fahimtar Nahawun Hausa a matsayin ka’idojin harshen da ake amfani da su wajen yin magana mai ma’ana. Wannan maganar tana iya kasancewa ta baka ce ko rubutacciya.

Ma’anar Ka’idojin Rubutu

Ka’idojin Rubutun Hausa na iya daukar ma’anar‚ ingantacciyar hanyar rubuta Hausa (Sa’id, B. 2004:1).

Shi ko Wurma (2005:ib), a kokarin bayyana ma’anar ka’idojin rubutu, ya danganta ka’idojin rubutun ne da Daidaitacciyar Hausa, inda ya fara da cewa‚ Hausa harshen ne wanda yake amfani da wasu ka’idoji na musamman a wajen rubutu. Ya ci gaba da cewa ‚Sau tari, mutane, wadanda ba su san wadannan ka’idoji ba kan bata rubuce-rubucensu ko maganganunsu ta hanyar kin bin wadannan ka’idoji.

Ke nan mutanen da suke bin wadannan ka’idoji, su ne ake cewa suna amfani da Daidaitacciyar Hausa.

Dangantakar Nahawu da Ka’idojin Rubutu

Kamar yadda Muhammad (2009), ya bayyana:

A ka’idojn rubutun Hausa, duk wanda bai san Nahawun Hausa ba, ko an gyara masa rubutun yau, gobe yana bata shi. Dalili shi ne dole marubuci ya kiyaye da tubulin Nahawun Hausa irin su bambancin suna da wakilin suna da sauransu. Misali a dokokin hade kalmomi akan ce ana hade kalmomin mallaka doguwa da gajeruwa. Bugu da kari, lamirin mallaka yana tare da abin da aka mallaka, a gajeruwa da doguwar ’yar mallaka.

Misalin gajeruwar ’yar mallaka:

  • Rigata
  • Gidansu
  • Hularsa
  • Kayansu

Misalan doguwar ’yar mallaka:

  • Gona tawa
  • Kudi namu

Da sauransu.

Dukkan wadannan, sai an shiga fagen Nahawu za a iya yi wa mai rubutu bayani ya gane. Wannan ya nuna mai koyon Ka’idojin Rubutun Hausa kamar yana koyon Nahawun Hausa ne. yana da kyau mai rubutun Hausa ya fahimci Nahawun sosai da sosai don hakan zai taimaka masa fahimtar Ka’idojin Rubutun Hausa.

Haka abin yake, Muhammad (2009) ya ce‚ ba aibi ba ne a ce Ka’idojin Rubutun Hausa sun taimaka matuka ga ci gaban Nahawun Hausa.

Bambancin Ma’ana a Tsakanin Kalmomin ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa

Samfurin Wasu Rubuce-Rubuce na Hausa

A kokarin kafa hujja a kan cewa ana amfani da wadanan kalmomi a rubutun Hausa na yau da kullun, ga sakamakon nazarin wasu rubuce-rubuce da aka yi. Za mu fara da wasu jaridun Hausa.

Jaridar Aminiya

A wata hira da wakilin jaridar ya yi da daya daga cikin ’yan takarar Gwamnan Jihar Kaduna, ga yadda jaridar ta rubuta bayanan dan takarar:

“Akwai ayyuka da za mu yi a nan ba kuma duka ayyukan da za mu yi ba ne jama’a za su so amma da yawan jama’a za su ji dadinsu. Idan har jama’a suka zabe mu ke nan suna neman canji. Ke nan ba su son jihar ta zama wajen kafa manyan fastoci amma babu aikin komai. Ke nan suna bukatar makarantu su inganta fiye da yadda suke a yanzu. Ke nan suna bukatar asibitocinmu su inganta yadda kowa zai amfana ba sai wanda ke da kusanci da gwamnati ba za a dauki nauyinsa zuwa kasar Masar neman magani. Jaridar Aminiya(2014:27).

A wata hira da jaridar (Aminiya 2014:10) ta yi da wani dan kasuwa, ga yadda rubutun(amsar da dan kasuwar ya bayar) ya kasance:

“Eh! Yauwa abin da nake nufi ke nan munufar ke nan. Kowa ya rika sanin irin maganganun da zai fada wa jama’a…..”

A kokarin amsa wata tambayar, dan kasuwar ya ci gaba da cewa: Abin da zan ce a kan wannan a wajen manyanmu, manyan ’yan siyasa ke nan ba mutanen jihar ba.”

A shafi na 25 a wata tattaunawar ta daban, ga tambayar da wakilin jaridar ya yi: “To amma ka san a Najeriya kafofin yada labarai da yawa ba sa biyan ma’aikatansu a irin wannan yanayi, yaya kake son ya yi ke nan?

A shafin Kimiyya da Kere-Kere, jaridar (2014:32) ta yi bayanin tsarin babbar manhajar Android(3). A sakin layi na hudu, ga yadda rubutun ya kasance:

Wannan babin da ke hada tsakaninsu kenan

Sannan kuma, a sakin layi na kusa da karshe, ga yadda jaridar ta yi rubutun:

Sai dai a bangaren babbar manhajar Android abin ya dan sha bamban, saboda sarkakiyar da ke cikin tsarin, da kuma muhallin da ake tsammanin kasancewarta a ciki bayan gina ta, wato wayar salula kenan.”

Jaridar Aminiya(2014:32)

A shafi na 18, ta ranar Juma’a 25 ga watan goma, 2019, ga abin da aka rubuta: “Ke nan ba Katsinawa kadai ba, Malam Zungur yana ishara ga dukkan al’ummar Arewa da su dauki wadannan halaye masu kyau, domin inganta rayuwarsu.”

Idan muka dubi rubuce-rubucen da aka gabatar a sama, za mu ga jaridar ta yi amfani da duka kalmomin(‘kenan’ da ‘ke nan’), to wanne ne ba wanne ba?

A littafin ‘Zahra’ wanda Madaba’ar Maizar ta wallafa(2007), a shafi na ashirin da biyu, ga abin da aka rubuta:

“Suka fashe da dariya. Adam ya tsagaita dariyar ya ce‚ ashe ka gano su kenan. To amma kuma mu suka dauka ba mu da wayo. Har suke ikirarin juya mu yadda suke so, haka ne ko?”

A shafi na ashirin da shida kuwa, ga abin da aka rubuta:

“Wallahi har kunyar fadi nake, saboda Allah in ke ce haka ta faru dake, za ki yarda? Ta yi ’yar dariya ta ce‚ Zahra kenan, zan yarda man, tunda yana da aikin yi.”

Wannan samfurin da ka bayar ya nuna mana cewa ana amfani da kalmomin ‘kenan’ da ‘ke nan’ a rubuce-rubucen Hausa. An yi hakan ne don kafa hujjar cewa tabbas ana amfani da wadannan kalmomi.

 

Aminu M.B. Umar

08036897982

[email protected]

Zamu ci gaba