✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangantakar Nahawu da Ka’idojin Rubutu (2):

Nazari a kan Bambancin Ma’ana a Tsakanin Kalmomin: ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa A wannan makon Aminiya ta kawo muku dangantaka da ke tsakanin…

Nazari a kan Bambancin Ma’ana a Tsakanin Kalmomin: ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa

A wannan makon Aminiya ta kawo muku dangantaka da ke tsakanin Nahawu da ka’idojin rubutu, wanda yake nazari ne a kan bambancin ma’ana a tsakanin kalmomin ‘Kenan’ da ‘Ke nan’ a Hausa. Malam Aminu M.B. Umar ne ya gabatar da mukalar a taron kara wa juna sani na kasa da kasa, da Jami’ar Jihar Kaduna ta shirya a ranar 14 zuwa 17 ga watan Nuwambar bara. A makon da ya gabata mun kawo muku nazarin da mai rubutun ya yi a kan ma’anar Nahawu da dangantakarsa da ka’idojin rubutu da kuma samfurin wasu rubuce-rubuce a kan kalmomin ‘Kenan’ da ‘Ke nan.’

Ma’anar Kalmar ‘kenan’

Kalmar ‘kenan’ kalma ce mai gaba biyu wadda ake amfani da ita a maimakon; ‘wannan na nufin’ da ‘hakan na nufin’ da ‘abin nufi’da kuma ‘ma’ana’.

Gaba ta daya budaddiya ce(BW). Gaba ta biyu kuma rufaffiya ce(BWB). Don karin bayani kan gabar kalma a Hausa, a duba Sani, (1999). Kenan, kalma ce da ta ke karfafa wani zance ko nuna muhimmancin zancen da aka yi. Tana kuma bayyana karshe ko kammalawar wani zance(Skinner, N. 1977).

Misali; wajen karfafa wani abu ko wani al’amari, watau don tabbatar da yadda abu yake ko yadda wata halitta ta ke, a kan ce:

  1. Mutum kenan: idan ana so a nuna ya aikata wani abin da ba a yi zatan zai aikata ba. Dubi dai yadda Dakta Mamman Shata ya kwatanta shi da ‘mugun ice’. Wanda za ka dasa, sai ya girma, har yai inuwa luf-luf-luf, gun shan inuwar ku yi tawaye… mutum kenan, mutum sai Allah.
  2. Rayuwa kenan: haka ita ma rayuwa tana faruwa kamar ba a yi ba. Komai mai zuwa ne ya zuce. Shi ya sa, a rayuwa, abin da ya ba ka tsoro, wata rana sai ya ba ka tausayi. Haka abin da ya ba ka tausayi, yana iya baka tsoro. Rayuwa kenan.

iii. Rabon kenan: duk da yake rabon kwado ba ya hawa sama, ko ya hau zai fado, mutum yakan nemi wani abu bai samu ba, sai kuma wani sanadi ya sa ya sami wani abin daban. Wannan abin nan na biyu da aka samu shi ne rabon. Watau rabon kenan.

  1. ib. Yaro kenan/kuruciya kenan: yaro kan yi wani abu na yarinta, sai a karfafa ko a tabbatar da matsayinsa na yaro da abin da zai iya aikatawa.
  2. b. Gwamnati kenan: haka ma idan ana tabbatar da ikon gwamnati kan wani al’amari ko wani aiki da ta yi ko wani hukunci da ta dauka, sai a ce gwamnati kenan. Watau za ta iya yin fiye da abin da ta yi.
  3. b Kudi kenan: duk dai samma-kal, domin batu ne karfafawa. Idan ka ga mutum da sutura kyakyawa yana yin yanga yana yin toroko, to ya samu kudi kenan. Kodayake, Dakta Mamman Shata ya ce ‚gumi nai yake ci. Da sauransu.

Wannan kalma ta kenan kan siffantu da ma’anar ‘ne’ da ‘ce’. Sai dai takan karfafa zance fiye da ‘ne’ da ‘ce’.

Misali:

Garba ne

Garba kenan

Mace ce

Mace kenan

A wajen bayyaana karshe ko kammalawar wani zance, akan ce:

  1. Shi kenan:

Ya mutu. Shi kenan.

Farantin ya fashe. Shi kenan.

Shi kenan, babu sauran wani kyan-kyan-kyan, mai kalangu ya fada rijiya.

Shi kenan, ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata.

 

Sharhi Kan ‘Ke nan’

‘Ke nan’, kalmomi ne guda biyu ‘ke’ da ‘nan’. kalmar ‘Ke’ na iya daukar ma’anoni biyu, Kalmar ‘nan’ kuma na iya daukar ma’anar wakilin suna nunau da kuma bayanau.

  1. Sani(2009), ya bayyana ‘ke’ da cewa wakilin suna ne mai cin gashin kai. Yana iya zama shi kadai ba tare da ya hadu da wani abu daban ba.

A Kamusun Hausa na Jami’ar Bayero(2006), an bayyana ‘ke’ a matsayin lamirin mace da ake magana da ita. Misali:

ke ‘yar’uwata ce.

Ke kanwata ce.

Ke, zo nan.

  1. A Kamusun Hausa na Jami’ar Bayero(2006), an bayyana ‘ke’ a matsayin harafi da ake hadawa da wakilin suna wajen bayyana aikin da ake cikin yi. Misali, a mataimakin fi’ili, Sa’id(2004).

Nake

Kake

Take

Suke

Muke

Idan aka shafe gaba ta farko (lamirin suna) na wadannan kalmomi na sama, sai alamar lokacin(Bello, A.) ta tsaya ita kadai. misali:

Ni nake magana. = Ni ke magana.

Kai ne kake surutu haka? = Kai ke surutu haka?

Ita ce take shara. = Ita ce ke shara.

Abubuwan da suke ciki. = Abubuwan da ke ciki

 

Sakamakon Bincike

Idan aka yi la’akari da ma’anar nahawu (Bello,2004 da Sani, 1999 da Muhammad,2009) da ma’anar ka’idojin rubutu(Sa’id, 2004:1 da Wurma, 2005:ib) da kuma dangantakar nahawu da ka’idojin rubutu(Muhammad,2009), za a iya fahimtar cewa Kalmar ‘kenan’ (a hade ba a rabe ba) ta fi dacewa da ma’anar; ‘wannan na nufin’ da ‘hakan na nufin’ da ‘abin nufi’ da ‘ma’ana’, a tsakanin ‘kenan’ da ‘ke nan’ , Skinner(1977:78).

 

Kammalawa

Wannan nazari ne a kan dangantakar nahawu da ka’idojin rubutu, nazari bambancin ma’ana a tsakanin kalmomin ‘kenan’ da ‘ke nan’ a Hausa. Kalmomi ne da ake amfani da su a maimakon a rubuta;‘wannan na nufin’ da ‘hakan na nufin’ da ‘abin nufi’ da kuma ‘ma’ana’. Sakamakon nazarinn shi ne amfani da kalmar ‘kenan’ ya fi dacewa. Sannnan kiyaye irin wadannan kalmomi na matukar amfani domin yin hakan zai taimaka wajen rubuta Hausa daidai, musamman idan aka yi la’akari da matsayin harshen a jiya da yau na burin zama harshen kasa a Nijeriya, gobe.

Daga Aminu M.B. Umar

08036897982

[email protected]