✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dangote zai gyara filin wasan MKO Abiola da ke Abuja

Ministan Matasa da Bunkasa Wasanni, Mista Sunday Dare a  ya ce attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote zai dauki nauyin gyara filin wasa na kasa da…

Ministan Matasa da Bunkasa Wasanni, Mista Sunday Dare a  ya ce attajirin Afirka Alhaji Aliko Dangote zai dauki nauyin gyara filin wasa na kasa da ke Abuja da ake fi sani da filin wasa na MKO Abiola.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din makon jiya a wani taro da ya yi da manema labarai. Ya ce attajirin zai daukin nauyin gyaran filin wasa ne ganin yadda filin ya lalace kuma abin kunya ne a ce ba a iya yin wasa a filin da ke Birnin Tarayya sai dai a kai wasu sassan kasar nan.

“Aliko Danogte ya bayyana niyyarsa ta gyara filin wasa na MKO Abiola, kuma ana sa ran zai fara aikin ne nan da mako daya ko biyu. Muna sa ran nan da watan Maris din badi za mu samu akalla filayen wasanni hudu masu kyau a kowane sashe na kasar nan,” inji shi.

Ministan ya ce, “Idan haka ta kasance babu shakka kasar nan za ta iya daukar nauyin wasannin da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) take shiryawa.”

Abubuwan da Dangote zai gyara a filin sun hada da dasa sabuwar ciyawa ta zamani da allon rubutu sakamakon wasa na zamani da samar da kujerun ’yan kallo na zamani da filitun da za su kawata filin da sauransu.

An dade ba a gudanar da wasan kwallon kafa a filin wasa na kasa da ke Abuja ba saboda lalacewarsa.