✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Dani Albes ya so ya ba ni zuciyarsa don a dasa mini -Eric Abidal

Tsohon dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Eric Abidal a ranar Talatar nan ne ya bayar da labarin da ya sosa zukatan magoya bayan…

 Eric AbidalTsohon dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen Eric Abidal a ranar Talatar nan ne ya bayar da labarin da ya sosa zukatan magoya bayan kulob din bayan ya shaida musu yadda tsananin abokantakarsu take a tsakaninsa da dan wasan baya a kulob din watau Dani Albes a lokacin da yake wasa a kulob din.
Hasalima, Abidal ya bayyana cewa a lokacin da Likitoci suka yi kokarin yi masa aiki a hantarsa wacce ya samu matsala a shekarar bara, dan kwallo Dani Albes ya shaida musu cewa idan ana bukatar ya bayar da gudunmawar hantarsa don a yi wa Abidal dashenta, a shirye yake da yin haka.
Ya ce abokantakar da ke tsakaninsa da Albes ta wuce misali, don ta wuce ta aboki ta koma ta dan uwa na jini.
Sanannen abu ne dai yadda ’yan kwallon biyu suka kulla aboka ta kut-da-kut a lokacin da suke tare a kulob din FC Barcelona.
Hakan ce ma ta sa Albes a yanzu haka ya koma amfani da rigar kwallo mai lamba 22 wacce Abidal ya taba yin amfani da ita a lokacin da yake kulob din don tabbatar wa duniya cewa har yanzu akwai alaka mai karfi a tsakaninsa da abokinsa Eric Abidal.
Eric Abidal, da yanzu haka yake buga kwallo a kulob din Monaco da ke Faransa, ya samu matsala a hantarsa a lokacin da yake wasa a kulob din FC Barcelona a shekarun baya ne inda ta kai sai da Likitoci suka yi masa dashen hanta kuma ya shafe lokaci mai tsawo yana jinya ba tare da ya buga kwallo ba.
A shekarar bara ce da ya samu sauki ya canza sheka zuwa Faransa don ci gaba da kwallo a kulob din Monaco.
Tun bayan yi masa aikin a shekarar bara sai a wannan lokaci ne dan kwallon ya fito karara ya bayyana halin da ya shiga da kuma irin taimakon da abokinsa Dani Albes ya yi masa a lokacin da suke tare a kulob din.
Abidal ya ce tsohon kocinsa Pep Guardiola ya yi yunkurin daukarsa zuwa kulob din Bayern Munich da ke Jamus amma kulob din ne ya ki amincewa da hakan saboda dashen hantar da aka yi masa da a tunaninsu zai iya samun matsala a nan gaba.