Categories: Iyayen Giji

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (10)

Bayan Dokta Samira ta samu juna biyu ne sai rayuwa ta canja, inda a kullum murna take yi za ta samu danta na farko da masoyinta Dokta Ibrahim.  A bangaren Dokta Ibrahim ma kullum sai murna da addu’a yake yi don ganin matarsa Samira ta sauka lafiya, don ya zaku ya ga abin da za ta haifa, shi ma ya zama uba.

Sai dai duk da cikin da Dokta Samira take dauke da shi, hakan bai hana ta ci gaba da kula da iyayen Ibrahim da suke zaune a gida daya ba, duk da suna sashinsu na daban.  Mahaifiyar Dokta Ibrahim wato Hajiya Delu takan yi murna da kuma alfahari kan yadda Dokta Samira take matukar kula da su.  Ko aikin gida ba ta barinta sai dai ita Samira ta yi da kanta. Hajiya Delu kan kwabe ta cewa tana fa dauke da juna biyu, ba ta ganin hakan zai iya janyo mata matsala?  Sai Dokta Samira ta amsa da cewa :Ai hakan shi ne daidai, ana son mai juna biyu ta rika motsa jiki don hakan zai yi matukar taimaka mata.  Hasali ma takan yi raha da Hajiya Delu cewa ko ta manta ita Likitan yara ce, ta san kabli da ba’adin kula da mai juna biyu?  Hajiya Delu kan yi murmushi ta ce lallai Dokta kin fi ni gaskiya don bangaren da kika karanta ne.

ADVERTISEMENT

Kwanci-tashi cikin Dokta Samira ya girma, inda aka ba ta hutu har sai ta haihu yaro ya fara kwari kafin ta koma aiki.  Hakan ya sa ta daina zuwa aiki, sai zaman gida kawai.

A kullum hankalin Dokta Ibrahim yana kan matarsa Dokta Samira, don haka yakan kira ta ta waya duk bayan minti 30 zuwa awa daya don ya ji halin da take ciki.  Takan sanar da shi babu komai, kuma idan akwai matsala za ta kira shi a waya ko ta turo a sanar da shi.

ADVERTISEMENT

Wata rana jim kadan bayan ta kammala Sallar Azahar sai nakuda ta kamata a gida, ba tare da sanin Hajiya Delu ba. Kukan jariri ne ya janyo hankalin Hajiya Delu inda ta  nufi dakin su Dokta Samira don ganin abin da ke faruwa. Da isarta ta tarar Dokta Samira ta haifi ’ya mace har ta yi namijin kokari wajen shirya kanta da jaririyar ba tare da taimakon wani ba.

Dokta Ibrahim ya koma ofis daga Sallar Azahar sai ga waya daga gida, aka sanar da shi matarsa Samira ta haifi ’ya mace.  Nan take  ya koma gida bayan ya sanar da sauran ma’aikatan asibitin.

Kafin ranar suna ta zagayo sai Hajiya Delu ta kira Dokta Ibrahim don su yi shawarar sunan da ya kamata a sanya wa jaririyar.  Ta ba shi shawarar a sanya sunan Halima, wato tsohuwar matarsa.  Nan take Dokta Ibrahim ya amince kuma ya sanar da Samira.  Ita ma ta ce hakan shi ne daidai duk da yake a zuciyarta ta so sanya sunan kakarta ce idan Ibrahim ya ba ta dama, amma saboda biyayya da kuma soyayyar da ke tsakaninta da Dokta Ibrahim ta amince da sunan Halima.

Bayan an yi shagalin suna an watse sai Dokta Ibrahim da Dokta Samira suka shiga hira a kan yadda rayuwa ta kasance musu tun daga haduwarsu a jami’a har zuwa daura musu aure har zuwa samun karuwar da suka yi ta haihuwar ’ya mace. Sai dai ya nuna mata duk da auren dole da aka yi masa a tsakaninsa da tsohuwar matarsa Halima, ba zai taba manta irin zaman mutunci da so da kaunar da suka yi ba. Hasali ma ya nuna yin biyayya ga iyayensa na amincewa da wancan aure ne ya janyo masa alheri a rayuwa, inda tamkar ya jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya, wato ya auri Halima sannan ya auri budurwar da suka yi soyayya tun a makaranta Dokta Samira. Sai ya hori matasa su rika yin biyayya ga iyayensu koda sun zartar musu da wani hukunci da ba su so ba, hakan zai sa Allah Ya ba su mafita kuma Ya sanya albarka a cikin al’amarin, kamar yadda ta faru da shi.

Mun kammala.

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805

. .

Recent Posts

Kirkiro Masarautun Kano: Kotu ta tsayar da ranar yanke hukunci

Babbar kotun jihar Kano ta tsayar da ranar 14 ga Nuwamba 2019, a matsayin ranar da za a yanke hukunci…

1 hour ago

An yi arangama tsakanin ‘yan Kwankwasiyya da Gandujiyya a Kano

Akalla mutum takwas ne suka samu raunuka yayin da aka lalata motoci 10 a yau Litinin lokacin da aka yi…

2 hours ago

Kotu ta daure direba kan zargin yi wa agolarsa ciki a Abuja

Wata Kotun lardi ta birnin tarayya da ke Garin Jiwa Abuja, ta bada umarnin tsare wani direba mai shekara 36…

5 hours ago

’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka 16 sun kashe ’yan banga 3 a Kaduna

Al'ummar Karamar hukumar Igabi da ke a jihar Kaduna sun waye gari cikin tashin hankali inda wasu ’yan bindiga suka…

5 hours ago

An rantsar da sabon Mataimakin Gwamnan Kogi

Duk an kammala shirye-shiryen rantsar da Edward Onoja a matsayin sabon Mataimakin Gwamnan jihar Kogi. Babban alkalin jihar Nasir Ajanah,…

11 hours ago

Yau Buhari zai ziyarci kasar Rasha don halartar taro

A yau Litinin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, zai ziyarci birnin Sochi a kasar Rasha don halartar taron  kwana uku wanda…

12 hours ago