✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Darasi ga masu kin amincewa da auren dole (9)

Bayan su Samira da mahaifiyarta da sauran kannenta biyu sun koma gida da kwana biyu, sai ta ci gaba da yin waya da masoyinta Dokta…

Bayan su Samira da mahaifiyarta da sauran kannenta biyu sun koma gida da kwana biyu, sai ta ci gaba da yin waya da masoyinta Dokta Ibrahim. Sannu a hankali ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai iyayen Samira suka bukaci Ibrahim ya tura magabata don a sanya ranar aure.

Nan take Ibrahim ya sanar da mahaifinsa Malam Usman halin da ake ciki, inda shi kuma ya sanar da matarsa Hajiya Delu.

Bayan sun yi shawara sai aka sanya ranar da za a kai wa iyayen Samira ziyara don a tsayar da maganar aure.  Da ranar ta zo ne Malam Usman ya wakilta wani amininsa tare da wadansu na kusa da shi don su wakilce shi zuwa garin su Samira don ganawa da iyayenta.

Dokta Ibrahim ne ya bayar da mota tare da direba don a kai su garin su Samira.

Sun isa garin kafin Sallar Azahar. Da yake direban Dokta Ibrahim ya san garin su Samira, kwatancen gidan su Samira bai yi masa wahala ba wajen ganowa.

Nan aka yi musu tarba ta arziki.  Mahaifin Dokta Samira Malam Kabir mutum ne mai saukin kai da sanin ya kamata.  Ya yi murna kwarai da ziyarar da iyalan Dokta Ibrahim suka kai masa. Tun kafin su isa ya sanar da ’yan uwansa don su tarbi iyalan Dokta Ibrahim don a tsayar da maganar aure.

Bayan sun yi Sallah an kawo musu abinci sun ci, sun sha ne, sai aka shiga gaisawa da fadin dalilin ziyarar tasu. Nan aka tsayar da maganar aure aka sanya rana.

Sai dai Dokta Ibrahim ya roki a sanya lokaci mai dan tsawo don ya samu damar karasa ginin da yake yi, don ya yanke shawarar idan ya auri Samira, to za su tare ne a sabon gidan da yake ginawa.  A ginin da yake yi, ya ware bangaren mahaifansa da bangarensa, don ya nuna ba zai iya yin rayuwa ba tare da mahaifansa suna kusa da shi ba.  “Duk duniya ba na da wadanda nake alfahari da ji da su irin iyayena”, haka Dokta Ibrahim yake fadi idan aka yi masa tambaya game da irin shakuwar da ya yi da mahaifansa.

Kwanci-tashi Dokta Ibrahim ya kammala gini, kuma har sun tare a gidan tare da mahaifansa kafin ma a daura masa aure da Samira.  Yadda mahaifin Ibrahim Malam Usman da mahaifiyarsa Hajiya Delu suka rika murna suna yi wa Dokta Ibrahim addu’a, abin ba ya misaltuwa. Sun yi godiya ga Allah da Ya ba su da mai ladabi da biyayya irin Ibrahim.

Kafin lokaci kankane, lokacin biki ya yi.  An sha shagali, abinka da auren likitoci kuma sanannu.  Jama’a sun yi cincirindo wajen halartar daurin auren,  kowa sai Allah sam-barka da fatan alheri yake yi game da wannan aure na masoya biyu.

Amarya ta tare a dakinta.  Da yake ta bar ainihin garin da take aiki sai ta nemi a canja mata wajen aiki zuwa asibitin su Dokta Ibrahim.  Hakan ya sa suka kasance suna aiki a asibiti daya.

Dokta Ibrahim ya kware ne a bangaren kula da marasa lafiya maza da mata yayin da Dokta Samira kuma ta kware a bangaren kula da lafiyar yara musamman jarirai da ’yan kasa da shekara 10.

Nan dai rayuwa ta canja wa Dokta Ibrahim da Dokta Samira.  Suka ci gaba da zaman aure cikin jin dadi da annashuwa.

Dokta Ibrayim a cikin zuciyarsa ya ce bai taba zaton zai sake samun macen da za ta kwantar masa da hankali bayan rasuwar matarsa Halima ba. Ya zaci Samira ta fada kogin soyayya da wani tun bayan da aka yi masa auren dole, ashe rabonsa ce, yau ga shi ta zama matarsa da yake matukar kauna.

Ba a dade ba sai Dokta Samira ta samu juna biyu. Kada ka ga yadda amarya da angonta da kuma iyayensu suke murna.  Abin ba ya misaltuwa.

Sai mako na gaba za mu ji yadda za ta kaya.

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805